Home Siyasa Zamu Sarrafa Ruwa Don Inganta Rayuwar ‘Yan Najeriya – Minista Goronyo

Zamu Sarrafa Ruwa Don Inganta Rayuwar ‘Yan Najeriya – Minista Goronyo

148
0
Minista Goronyo 2

Ministan Ruwa da Tsaftar Muhalli, Hon. Bello M. Goronyo ya sha alwashin ganin cewa ya gudanar da ma’aikatarsa ta hanyar da zata inganta rayuwar Yan’Najeriya wajen anfani da ruwa ta hanyoyin da za su kawo cigaba da bunkasa tattalin arziki a kasarnan.

Ministan ya sanar da haka ne a hirarsa da Yan Jaridu bayan ya ziyarce ofishinsa dake Area 1, Abuja ranar Talata.

Hon. Goronyo ya ce ruwa shine rayuwa; wanda ya ce ruwa ya taba dukkan sassan dan adam; sabo da haka za su sarrafa shi domin inganta ruyuwar dukkan Yan Najeriya ba tare da la’akari da ga inda suka fito ba.

Ya ce shi da daya Ministan ruwa za su hada kai wajen ganin sun kawowa ‘Yan Najeriya cigaba ta fannin yin amfani da ruwa da kuma da samar da tsaftaceccen muhalli da za’a yi alfahari da shi a kasarnan.

Goronyo ya sha alwashin bayar da duk gudunmawar da ta dace wajen ganin an kawo cigaban da ya dace wajen ganin an inganta rayuwar Yan Najeriya ba tare da la’akari da banbancin addina ko kabila ba.

Minista Goronyo G

Sabo da haka, ya yi kira ga ‘Yan Najeriya da su ba su dukkan hadin kai da ya kamata da addu’o’I wajen ganin sun sami nasara akan aikin da suka sa a gaba don amfanar kowa da kowa.

Ministan ya godewa Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya zabe shi a matsayin daya daga cikin Ministocinsa domin bayar da gudunmawa da zata kawo cigaba ga ‘Yan Najeriya.

Har ila yau, ya godewa Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako wanda shine ya bayar da sunansa aka nada shi a Minista. Goronyo ya yi alkawarin ganin cewa bazai ba su kunya ba wajen sauke nauyin da yake kansa.

Da ga karshe ya yi kira ga ‘Yan Najeriya da su taya su da addu’a wajen ganin sun sauke nauyin da suka dauka. Inda ya yi alkawarin ganin ya yi aiki tukuru don inganta rayuwar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here