Home Addini Zamu Cigaba Da Aurar Da Zawarawa Domin Raya Sunnar Ma’aiki – Hon....

Zamu Cigaba Da Aurar Da Zawarawa Domin Raya Sunnar Ma’aiki – Hon. Mai Palace

177
0
Hon. Mai Palace

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Gusau/ Tsafe da ga Jihar Zamfara Hon. Kabiru Amadu Mai Palace, ya ce za su aurar da zawarawa 30 a cikin watan Janairu kuma tsari ne da za su cigaba da shi a wani mataki na tallafawa marasa gata a yankin sa.

Dan Majalisar ya fadi haka ne a hirarsa da Yan Jaridu a ofshin sa da ke Majalisar Wakilai da ke Birnin Taraiya Abuja a ranar Juma’a da ta gabata.

Hon. Palace  ya ce watan da ya gabata sun aurar da zawarawa 19 kuma ba shi ne na farko ba su na yi ne gwargwadon bukatar da aka gabatar ma sa bayan Yan Kwamitin Mata na yankin na sa sun gama tantancewa kuma sun gabatar masa da su.

Mai palace ya kara da cewa bayan sun aurar da zawarawan su na yi musu goma ta arziki tare da ba su kayan sana’a a wani mataki na ganin an sami zaman lafiya bayan an yi auren.

Abubuwan da su ke rabawa matan da su ka aurar sun hada da Firji domin yin sana’a wancce ta ke da alaka da kayan sanyi da kekunan dinki da kuma injin Nika sa bo da su dogara da kan su ba tare da sun matsawa mazajen su ba idan su na da wata bukata.

Dan Majalisar ya ce wadanda ba a zo kan su ba su kara hakuri domin kuwa shirin za a cigaba da shi a wani mataki na bayar da gudunmawa na raya sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

A wani bangaren kuma, Hon. Mai Palace ya yabawa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ga me da Kasafin Kudin da ya gabatar a gaban Majalisar Taraiya in da ya ce kasafin kudin ya kun shi tanade-tanade da za su inganta rayuwar talakawan Najeriya.

Mai Palace ku ma ya lura cewa Shugaban kasar ya gina kasafin kudin ne akan tsari na gaskiya domin da ga bayannan sa babu karya inda ya bayar da misali da farashin Dala in da ya sakata akan Naira 750 ya ce babu karya a ciki lura da yadda abubuwa su ke faruwa a kasarnan da ma duniya ba ki daya.

Da ga karshe ya ce abun jira anan shine a jira a ga gundurin kasafin kudin domin a ga yadda aka warewa kowanne bangare, in da ya ce haka shi zai ba da haske aga ko an yi kowanne bangare adalci ko a’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here