Home Kotu da 'Yan sanda Zamba Ta Kafar Sadarwa: An Kama Mutane 23 A Sokoto

Zamba Ta Kafar Sadarwa: An Kama Mutane 23 A Sokoto

133
0
EFCC Operatives

An kama mutane 23 da ake tuhuma da aikata ayyukan zamba da yaudara ta amfani da hanyar sadarwa ta intanet, a arewacin Najeriya, wanda hakan ke nuna yadda wannan dabi’ar ke ci gaba da yaduwa a sassan kasar.

Ranar Jumu’ar da ta gabata ne hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC ta ce ta kama wasu mutane 23 da take tuhuma da ayyukan zamba ta amfani da kafar sadarwa ta intanet a Sakkwato da ke arewa masu yammacin Najeriya.

Mutanen da ta kama da suka kasance daga manyan kabilun Najeriya. An lura da yadda suke bushasha da kudi abin da ya saba wa hankali, don haka ya sa hukumar ta yi musu dirar mikiya ta kama su, kuma tana kan bincikensu, kafin ta gudanar da su gaban kuliya idan ta same su da laifi.

Muryar Amurka ta yi kokarin ta ji ta bakin hukumar ta wajen kakakinta Kamilu Ibrahim, amma abin ya ci tura.

Mai sharhi akan lamurran yau da kullum kamar Malam Bashir Achida na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato na ganin wannan abu ne mai illa sosai.

Masanin sadarwar yanar intanet kuma babban sakatare na ma’aikatar da ke kula da fasahar sadarwar zamani a Sakkwato Nasir Daniya ya ce laifukan da ake aikatawa ta yanar intanet suna da yawa kuma sukan zo ta sigogi mabambanta.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da aka kama masu wannan dabi’ar a Najeriya musamman a kudancin kasar abinda jama’a ke ganin yana da kyau mahukunta su kara tashi tsaye wajen maganin matsalolin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here