Home Uncategorized Zamanantar Da Noma Ita Ce Manufar Mu Ta Samar Da Makarantar Aikin...

Zamanantar Da Noma Ita Ce Manufar Mu Ta Samar Da Makarantar Aikin Gona Da Kimiyya A Misau – In ji Hon. Bappa

111
0
Hon. Misau 2

An baiyana cewa samar da Makarantar aikin Nomo da Kimiyya a Misau wata dabara ta samar da kwararru wadanda za su zamanantar da sana’ar Noma a yankin Arewa maso  Gabas da ma Najeriya baki daya a wani yunkuri na bunkasa kasa da abinci.

Hon. Aliyu Bappa Misau dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar kananan hukumomin Misau da Dambam da ga Jihar Bauchi ne ya sanar da haka jimkadan da kammala taron jin bahasin jama’a akan Kudurin Kafa makarantar da ya gudana zauren Majalisar Wakilai a jiya Juma’a.

Ya ce ya lura da cewa yankin Arewa maso Gabas ba shi da makaranta wacce za ta rinka horar da manoma akan daburu na aikin gona na zamani duk da cewa Noma shi ne kashin bayan mutanen yankin shi ya sa ya nemi Majalisar Taraiya da ta sahale a kafa wannan makaranta.

A halin yanzu Kudurin ya samu amincewar Majalisar Wakilai in da har ya shallake karatu na daya da na biyu; wanda taron jin bahasin jama’ar zai bawa Kudurin dama ya shallake karatu na uku don ya zama Doka da zarar Shugaban Kasa ya saka mata hannu.

Hon. Misau ya kara da cewa yankin Misau ya shawara wajen aikin noma tun kafin zuwan turawa wanda hakan ya sa aka taba kafa makarantar kula ta bishiyoyi da kuma auduga amma babu cikakkiyar makarantar koyar da aikin Noma, shi ya sa suka bukaci da a kafa makarantar don bunkasa harkar.

Ya ce yankin ya na samar da rake da wake da gyada  da shinkafa da alkama da gero da dawa da sauran kayan amfanin gona wadan da ake fitar da su mota-mota. Wanda ya ce a kowacce rana a na iya fitar da motar rake sama da guda ashirin a kowacce rana da ga garin Misau kawai.

Bayan haka, Hon. Misau ya ce a duka yankin Arewa maso Gabas babu Makaranta ta aikin Noma duk da cewa yankin yayi fice wajen samar da abinci ga Najeriya baki daya.

Dan Majalisar ya kara da cewa yankin ya na da duk abubuwan da ake bukata da zai tallafawa Makarantar wajen bincike ta yadda za’a bunkasa harkar Noma na rani da na damina domin akwai Tafkin Diya da na Maladumba wadanda su ke samar da ruwa wajen noman rani.

Bayan wadannan akwai manyan Kamfanoni da su ke sarrafa kayayyakin da aka noma irin su auduga da Shinkafa da rake da gyada da sauran su. In da ya kara da cewa Misau ta zama wata karamar Najeriya ce tunda kabilu da yawa na Najeriya sun maida ita garin su irin su Igbo da  Yoruba da sauran kananan kabilu sun zama yan kasa.

Hon. Bappa Misau ya ce Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya yi alkawarin bayar da duk gudunmawar da ake bukata wajen ganin makarantar ta tabbata ta hanyar yin magana da sauran Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas da Yan Majalisar su dama Shugaban Kasa wajen ganin ya amince ya saka hannu akan kudurin da zarar ya je gaban sa.

Ya  ce Shugaban Karamar Hukumar Misau tuni ya bayar da gudunmawar fili mai girman kadada 2,500; bayan haka, kwararru da su ke yankin su ma sun yi alkawarin bayar da ta su gudunmawar wanda da ga cikin su ne ya bayar da shawarar a kara harkar yanayi ‘climate change’ a cikin sunan makarantar.

Ga me da batum yadda za’a samu kudade da ake bukata don gudanar da makarantar, ya ce hikimar shigo da maganar yanayi ciki shine akwai kungiyoyi na kasashen waje da su ke bayar da tallafi wajen binciken yanayi wanda hakan zai tallafa wajen samun kudade ga makarantar kuma Gwamnatin Taraiya ma tana bayar da kudade wajen gina makaratar. Bayan haka mutanen yankin ma ba za a bar su a baya su ma.

Yanzu abun da ya rage a gani shi ne a gabatar da rahoton jin bahasin jama’a da aka gudanar ga zauren Majalisar in da dukkanin Majalisun guda biyu Dattawa da ta Wakilai za su cimma matsaya kafin da ga bisani a amince da Dokar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here