Home Siyasa Zaben Shugaban Kasa: Dalilin INEC Na Dage Fadar Sakamakon

Zaben Shugaban Kasa: Dalilin INEC Na Dage Fadar Sakamakon

285
0

Hukumar zabe ta sanar da dage karba da sanar da sakamakon zaben shugaban ƙasa daga jihohi da take yi a babbar cibiyar sanarwar da ke Abuja, har zuwa karfe takwas na daren yau Litinin..

Shugaban INEC Farfesa Mahood Yakubu ne ya sanar da tafiya hutun, bayan sanar da sakamakon jihohi tara a yau, amma goma jumulla har da Ekiti a jiya.

Jihohin da aka kammala bayyana sakamakon nasu na zaben shugaban kasa daga cikin 36 zuwa yanzu su ne;

1- Ekiti inda dan takarar APC Bola Tinubu ya samu nasara da kuri’u 201,494

2- Osun inda dan takarar PDP Atiku Abubakar ya yi nasara da kuria’a 354,366

3- Ogun inda dan takarar APC Bola Tinubu ya samu nasara da 341,554

4- Ondo dan takarar APC Bola Tinubu ya yi nasara da kuri’u 369,924

5- Kwara dan takarar APC Bola Tinubu ya yi nasara da kuri’u 263,572

6- Yobe dan takarar PDP Atiku Abubakar ya yi nasara da 198,567

7- Oyo dan takarar APC Bola Tinubu ya yi nasara da kuri’u 449,884

8- Gombe dan takarar PDP Atiku Abubakar ya yi nasara da 319,123

9- Lagos inda dan takarar LP Peter Obi ya yi nasara da kuri’u 582,454

10- Enugu inda dan takarar LP Peter Obi ya yi nasara da kuri’u 428,640

APC ta lashe kujerun sanata uku a Katsina amma Atiku ya doke Tinubu

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Katsina ta bayyana cewa jam’iyyar PDP ce ta lashe zaɓen shugaban ƙasa bayan samun ƙuri’u mafi rinjaye.

Sai dai a ɓangare guda jam’iyyar APC mai mulki ce ta lashe dukkanin kujerun majalisar dattijai, wato na yankin Daura, da Katsina ta tsakiya da kuma shiyyar Funtua.

A ɓangaren majalisar wakilan tarayya kuwa jam’iyyar PDP ce ta lashe kujeru tara daga cikin 15.

Atiku ya ci zaben Shugaban Kasa a Adamawa

Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi nasara a jiharsa ta Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar ce ta sanar da sakamakon a Yola, babban birnin jihar.

INEC ɗin ta bayyana cewa Atiku ya ci zaɓe a jihar ne bayan samun kuri’u 417, 611, inda ya buge abokin takararsa na APC wanda ya zo na biyu da kuri’u 182, 881.

Peter Obi na jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da kuri’a 105, 648.

Wakilan PDP da na LP sun fice daga wajen tattara sakamakon shugaban ƙasa a Abuja

Wakilan jam’iyyun PDP da na Labour Party sun fice daga wajen ɗakin da ake tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa dake gudana a babban birnin ƙasar Abuja.

Kimanin wakilan jam’iyyu 10 ne suka fice daga ɗakin bayan shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya mayar da martani kan ƙorafe-ƙorafen da wakilan suka yi, kan yadda ake tattara sakamakon.

Sun nemi shugaban na INEC ya ba da umarnin sanya duka sakamakon jihohi a shafin intanet na hukumar ta zaɓe, kamar yadda aka tsara.

Shugaban na INEC ya bayyana musu cewa, za a duba duk wasu ƙorafe-ƙorafe da jam’iyyu suka gabatar, amma kamar yadda yake bisa doka, za a yi hakan ne bayan tattara sakamako.

Ficewar ta su alama ce ta nuna cewa ba su gamsu da bayanin da Farfesa Mahmud Yakubu ya yi musu ba.

Jama’a sun yi zanga-zanga saboda zargin maguɗin zaɓe a jihar Ebonyi

 Wani gungun matasa ya yi dafifi a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi domin gudanar da zanga-zanga kan zargin an tafka maguɗi a zaben shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki a jihar.

Lamarin na zuwa ne yayin da hukumar zaɓe INEC ta sanar da sakamakon zaɓen sanatoci da na ƴan majalisar wakilai.

Waɗanda suka gudanar da gangamin sun haɗa da magoya bayan tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Sam Egwu da sauran magoya bayan ƴan takara kamar Micheal Amannachi da Linus Okorie da Laz Nweru Ogbe da Eze Emmanuel.

Sun yi zargin cewa an fara yin zaɓen cikin lumana amma daga bisani kuma labari ya sha banban inda maguɗi ya shigo ciki.

Masu zanga-zangar sun yi kira ga INEC da ta gaggauta ɗaukan mataki tare da sanar da sahihin sakamakon zaɓen da aka gudanar a yankunan Ebonyi domin kare afkuwar tashin hankali.

Mrs Paulin Onyekachi, Shugabar INEC a jihar ta Ebonyi, ta yi kira ga masu zanga-zangar da su rungumi zaman lafiya. (BBC)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here