Home Siyasa Zaben Cika Gurbi A Jihar Kaduna: Ya Gudana Lafiya, Sai Dai...

Zaben Cika Gurbi A Jihar Kaduna: Ya Gudana Lafiya, Sai Dai Mun Gaji Da Gafara Sa … In Ji Ma Su Kada Kuri’a

150
0
20240203 094717

Zaben cika gurbi na yan Majalisar Taraiya ya gudana a Jihar Kaduna cikin kwanciyar hankali sai dai ma su kada  kuri’a sun nu na rashin gamsuwar su wajen sharbar roman Demokradiyya.

Hukumar zabe mai zaman Kanta wato INEC da Jimi’an tsaro sun shirya tsaf domin ganin cewa zaben ya gudana ba tare da wata matsala ba.
20240203 094846
Hukumar zabe ta INEC ta samar da kayayyakin zabe da jimi’an ta akan lokaci a dukkan  mazabun da a ka a gudanar da zaben na cika  gurbi a jihar.
Suma jami’an tsaro ba a bar su a baya ba inda su ka samar da wadatattun jaimi’ai tare da kayan aiki wadatattu a wuraren zabe.
20240203 114317
Daya da ga cikin yan takarar  Yusuf Ibrahim Zailani da ga Rigacikin da ke mazabar karamar hukumar Igabi ya kada kuriarsa da misalin 9:30 am cilin kwanciyar hankali ba tare wata matsala ba.
A Mazabar Cikun zaben ma ya gudana cikin kwanciyar hankali ba bu hayaniya sai dai masu  kada kurì’a ba su fito solar  ba duk da cewa hukumar zaben da ta Yansanda sun samar da abubuwan da ake bukata.
20240203 112925
Engr. Kamilu Sale ya nuna gamsuwar sa game da yadda zaben ya ke tafiya cikin tsari da kwanciyar hankali sai ya ce rashin Fitowar  ma su zabe wani abu ne wanda ba sabon  abu ba. In da ya ce gwamnati ta yi abun da ya kamata sabo  da haka idan jama’a ba su fito ba laifin su ne.
Shima Tsohon Ministan Noma Dr. Mahmud  Abubakar ya nuna gamsuwar sa da yadda zaben ya ke gudana ba bu wata matsala ko barazana ta tsaro a wurin  zaben.
Ya ce mutanen Cikin sun fito domin kada kuri’a ba kamar yadda ya ke ba a baya inda ya ce dukkan nin jam’iyun su na wurin ba ba bu wata matsala sabanin yadda ya ke faruwa a baya.
Dr. Mahmud ya ce wannan abun, a ya ba ne kuma ya ja hankalin ma su kada kuri’a da su yi cikin tsari ba tare da hatsaniya ba.
20240203 112546
Bar. Lawan Ismail wanda aka fi sani da Bola Ige dan Majalisa da ga Mazabar Zaria shi ma ya nu na gamsuwar sa ga me da yadda zaben ya gudana in da ya ce ko mai ya na tafiya kamar yadda a ka tsara.
A na gudanar da zaben zaben  cike gurbi ne a Kaduuna a kanan hukumomi guda bakwai kamar haka Chikun, Igabi, Kachia, Kaduna South, Kagarko, Kudan, da Kauru.
Har ya zuwa wannan lokaci da mu ke hada rahoton komai ya na gudana cikin kwanciyar hankali ba bu hayaniya sai dai mafi yawancin ma su kada kuri’a ba su fito ba a mazabar Cikun da wasu ma kananan hukumomin.
A ya yin da da a mazabar Igabi an sami fitowar ma su kada kuri’a kwarai da gaske wanda hakan a ka alakan ta shi da waye wa ta siyasa da mutanen yankin  suke da dashi.
Engr. Kailani Muhammad daya da ga cikin jiga jigan yan siyasa a jamiyar APC ya yabawa Hukumar Zabe mai zaman kan ta in da ya ce ta ta yi duk abun da ya kamata na  samar da kayan aiki da jami’an ta a kan lokaci.
20240203 145820
Ya ce Hukumar Yansanda ma ta yi rawar gani na bayar ingantaccen tsaro a jihar in da ya ce ko ina an tanade su ta re  da kayan aiki wanda hakan ya taimaka wajen gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
A tattaunawa da ma su kada kuri’a a in da Jaridar Viewfinder ta zagaya sun nuna rashin gamsuwar su da yarda ake gudanar  da siyasa in da su ka ce su da su ke kada kuri’a su na cikin yunwa su kuma yan Siyasa na sharaholiyar su.
In da su ka ce talauci ya yi masu katutu ba su da ababen more rayuwa kamar ruwan sha da tituna ma su kyau da makarantu da asibitoci in da su ka ce kullum sai alkawarin da ba sa cikawa shi ya sa ba su fito wajen kada kuri’a ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here