Home Siyasa Zaben Adamawa: Kotu Ta Kori Karar Da Binani Ta Shigar

Zaben Adamawa: Kotu Ta Kori Karar Da Binani Ta Shigar

191
0

Babbar Kotun ariya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ’yar takarar Gwamnan Jihar Adamawa a Jam’iyyar APC a zaben da aka kammala, Aisha Binani a shigar.

Sanata Aisha Binani a shigar da karar ne ana kalubalanar nasarar Gwamna Ahamdu Fintiri na jam’iyyar PDP a zaben.

Ta garzaya kotun ne tana neman kotun ta tabbatar da ita a matsayin zababbiyar gwamnan jihar kamar yadda kwamishinan zaben jihar da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari ya sanar da farko, ba bisa ka’ida ba.

Kafin nan, Binani a shigar da karar neman kotun ta hana Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) soke sanarwar da Hudu ya yi.

Sai dai a zaman Babbar Kotun Tarayyya da ke Abuja a ranar Laraba, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da bukatar.

Idan za a tuna sanarwar da Hudu ya yi ba bisa ka’ida ba ta sa INEC ta dakatar da shi tare da umartar jami’an tsaro su bincike shi, lamarin da  ya sa ya shiga buya.

Tuni INEC ta bayyana sanarwar da ya yi alhali ana tsaka da tattara sakamakon zabe, ta kuma ce ba huruminsa ba ne sanar da sakamakon zabe.

Daga bisani bayan tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 11 da suka rage a zaben, jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Mohammed Mele, ya sanar cewa Gwamnan Fintiri na PDP ne ya yi nasara. (Aminiya).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here