Home Diplomasiyya Zaben 2023: Gwamnati Ta Bada Umarnin Rufe Iyakokin Najeriya A Ranar Asabar

Zaben 2023: Gwamnati Ta Bada Umarnin Rufe Iyakokin Najeriya A Ranar Asabar

212
0

Yayin da ‘yan Najeriya ke shirin gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar taryya a ranar Asabar, gwamnatin tarayyar ta bada umarnin rufe dukkan iyakokin kasa na kasar.

Shugaban ma’aikatar shige da fice ta Najeriya, NIS, Isah Idris Jere shine ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fita da yammacin Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Shugaban na migireshi na kasa ya ce za za rufe kan iyakokin ne daga ranar Asabar zuwa Lahadi.

An fitar da sanarwar ce kamar haka, Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe duk iyakokin kasa daga karfe 12 na safiya a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023 zuwa karfe 12 na safiya a ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairun shekarar 2023.

A dan haka sanarwar ta ce, duk wani kwamanda ma’aikatar musamman wadanda ke jihohin dake kan iyaka su tabbatar da ganin an bi umarnin daidai-wa-deda. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here