Home Siyasa Za mu magance rikicin shugabanci – PDP

Za mu magance rikicin shugabanci – PDP

101
0
PDP Flag

A yau Alhamis din nan ne babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, za ta gudanar da taron majalisar zartarwarta na kasa a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

A lokacin za a tattauna batun shugabancin jam’iyyar, wanda ya dade yana hannun riko, da dimbin matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar, da kuma shawarwari kan yadda za a ciyar da ita gaba.

Babban taron zai kasance ne yayin da wani rikicin cikin gida ya turnuke a cikin jam’iyyar.

Ana kuma sa ran zai sami halartar kusoshin jam’iyyar daga sassa daban-daban na kasar.

An kwashe wata da watanni ana ta dakon taron kwamitin kolin babbar jam’iyyar hamayyar.

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar, Ibrahim Abdullahi ya ce an shirya tsaf don gudanar da wannan taro, inda za a tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar.

Ibrahim ya ce za a ji ƙorafe-ƙorafe da ke akwai a jihohi da ƙasa gaba daya domin samar da hanyar da za a ciyar da jam’iyyar gaba, musamman abin da ya shafi haɗin kanta.

Ana hangen mai yiwuwa za a gudanar da zaben sabon shugaban jam’iyyar ta PDP, a wannan taro na Alhamis, sai dai mai magana da yawun jamn’iyyar ya ce : ” Babu hurumin a yi zaɓe yanzu, sai 2025, lokacin da wa’adin wannan kwamitin zai ƙare.”

Taron majalisar zartarwar yana zuwa ne yayin da kurar rikici ta mamaye jam’iyyar, har ana zargin ana wata asakala ta kokarin karbe shugabancin jam’iyyar tsakanin bangaren tsohon matamakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar da na ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Ibrahim Abdullahi ya ce tuni jam’iyyar ta kafa kwamitin yin sulhu tsakanin jagororin jam’iyyar.(BBC)

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here