Home Kotu da 'Yan sanda Za mu farfaɗo da yardar ‘yan Najeriya a kan ‘yan sanda –...

Za mu farfaɗo da yardar ‘yan Najeriya a kan ‘yan sanda – Babban Sufeto na riƙo

278
0
Sabon IGP

Sabon babban sufeton ‘yan sandan Najeriya na riƙo, Olukayode Adeolu Egbetokun ya ƙaddamar da abin da ya kira tsare-tsaren aiki don farfaɗo da yardar jama’a a kan ‘yan sanda.

Babban sufeton ya ƙaddamar da sabbin manufofin ne yayin wani taron ƙaddamar da salon shugabancinsa a shalkwatar ‘yan sanda ta ƙasa da ke Abuja.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce a cikin manufofin babban sufeton akwai kafa jami’an kai ɗauki cikin hanzari mai taken Quick Intervention Squad wanda zai haɗar da ‘yan sandan kwantar da tarzoma da za su kasance shiri don kashe wutar fitintinu da aikata laifuka.

Ya kuma ce shugabancinsa zai tabbatar da aiki da fasahohin zamani kamar ƙididdigar alƙaluma da harkokin tattara bayanan sirri don bunƙasa ƙwazon ‘yan sanda.

Haka kuma, babban sufeton zai tabbatar da aiki da wani tsarin martabawa da ba da lada don ƙara ƙwazo da ƙarfafa gwiwar jajirtattun jai’an rundunar. Yayin taron na ranar Juma’a manyan jami’an ‘yan sandan Najeriya daga faɗin ƙasar ne suka halarta.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne a ranar Litinin ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron ƙasar, a ciki har da Olukayode Egbetokun a matsayin babban sufeton ‘yan sanda na riƙo (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here