Home Labaru masu ratsa Zuciya Za A Rataye Mutum 3 A Jigawa Saboda Aikata Kisan Kai

Za A Rataye Mutum 3 A Jigawa Saboda Aikata Kisan Kai

224
0

Wata babbar kotu da ke Kaugama a Jihar Jigawa ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin kisan kai da aikata fashi da makami.

Kotun dai ta sami Suleiman Bello da Auwalu Muhammed da kuma Yakubu Muhammed da laifin kashe wani mai suna Audu Saje, mazaunin kauyen Manda na Karamar Hukumar, sannan suka gudu da babur dinsa.

Kazalika, kotun ta same su da laifin sace wata mata mai suna Hadiza Abdullahi ta garin Marma da ke Karamar Hukumar Kirikasamma, sannan suka nemi a biya su fansar Naira miliyan 150.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a M. M. Kaugama, ya ce masu shigar da kara, bisa jagorancin Babban Lauyan Gwamnatin Jihar, Dokta, Musa Adamu Aliyu, sun gamsar da kotun cewa mutanen da ake zargi sun aikata laifukan.

Sai dai kotun ta saki tare da wanke mutum na biyu a cikin wadanda ake zargin, Ya’u Mai Hatsi daga dukkan zarge-zargen. (Aminiya).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here