Home Tsaro Yansandan Jihohi: Yadda Masu Ruwa Da Tsaki Su Ka Baiyana Mabanbantan Ra’ayoyi

Yansandan Jihohi: Yadda Masu Ruwa Da Tsaki Su Ka Baiyana Mabanbantan Ra’ayoyi

175
0
IMG 20240422 WA0124
Mahalantar Taron Kan kirkiro Yansandan Jihohi sun nu na ra’ayi mabanbantan akan yiwuwar  samar da hukumar ganin Yadda Gwamnoni ka iya yin  amfani da wannan dama don cimma bukatun su na siyasa.
Taron wanda Majalisar Wakilai ta shirya Jiya Litinin karkashin jagorancin Kakakin ta  Dr. Tajudeen Abbas ya sami halartar mutane da ga ciki da wajen Najeriya.
Tsohon Shugaban Najeriya, Abdulsalami Abubakar a nasa ra’ayin cewa ya yi Yansnandan Jihohi za su yi tasiri ne kawai idan za ayi Shugabanci a bisa tsari na gaskiya da adalci.
Inda ya ce adalci da gaskiya da rikon amana su ne kashin bayan Shugabanci ba tare da la’akari da bangaranci da addoni ko kabila ba wajen gudanar wannan tsari.
Ya kara da cewa muddin Shugabanni ba za su yi  adalci ba a mat akin Jihohi za su yi  kama karya ne to lallai kuwa samar da Yansandan Jihohi zai kara ta’azzara abubuwa ne kawai.
A nasa bangaren tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ya ce babu kokonto akan bukatar Yansandan Jihohi a Najeriya sai dai in da matsalar ta ke ita ce ta yaya za a gudanar da su ba tare da son zuciya ba.
Jonathan ya ce lokacin da ya na Gwamna  a jihar sa ta Bayelsa ya fuskaci barazanar tsaro mai yawa amma da ya fito da tsari na yan sa kai ya sami nasarar shawo kan matsalar cikin sauri.
Shugaban ya shawarci wadanda su ka shirya taron da su mayar da hankalin su wajen lalubo hanyoyi da za su hana yin amfani da Yansandan wajen cika buri na yan siyasa da yadda za a aiwatar da tsarin ba tare   son zuciya ba.
Hon. Sada Soli daga Jihar Katsina cewa ya yi wannan taro yunkuri ne na yin gyara akan Kundin Tsarin Mulki na Kasa domin ya bawa Jihohi dama da su kirkio da Yansandan Jihohi na kan su sakamakon barazanar tsaro da ta addabe su.
Dan Majalisar ya ce ya na da ra’ayi kala biyu akan samar da wannan Doka lura da bukatar da ake da ita. Ya ce sai an duba alfanu ko rashin alfanun samar da Yansandan ta hanyar tantance yadda za a yi amfani da su ba tare da son zuciya ba.
Ya  ce  makasudin taron shine don aji ra’ayin jama’a don a fahimci yiwuwar samar da Yansandan ko kuma a’a. Amma kuma Dokar ba zata tabbata ba sai an sami amincewar kananan hukumomi 24 da ga cikin 36 da ke kasarnan.
Shima Hon. Halliru Jika tsohon Dan Majalisar Taraiya da ga Jihar Bauchi kuma Shugaban Kwamitin Yansanda cewa ya yi taron ya zo a lokacin da ya dace duba da yadda kasarnan ta ke fuskantar barazanar tsaro.
Sai ya bayar da shawarar ayi taka tsantsan wajen gani ba a yi amfani da Yansandan ba wajen musgunawa yan adawa na siyasa a jihohin.
Wani Kwararre akan tsaro Dr. Kabiru Adamu cewa ya yi wannan batum samar da Yansandan Jihohi ba sabon abu bane domin an taba samar da su a janhuriya ta farko amma aka dakatar da shi sakamakon matsaloli da aka fuskanta.
Ya ca a wannan karon ma bukatar ta bijiro ne a sa kamakon tabarbarewar tsaro a jihohin sai dai akwai tsoron cewa Yan Siyasa ka iya yin ammafi da su don musgunawa abokan adawa.
Masana da yawa da suka halarci taron sun nuna mabanbantan ra’ayi wajen waye yake da alhakin samar kudade da Shugabanci, ko horasswa ko makiamai ko kayan Yansandan a jihohin da sauran gudanarwa.
Su ka ce wadannan wa su batutuwa ne da suke da bukatar da a yi nazari akan su kafin a amince da wannan Doka.
Suma Wakilai da ga Kasashen Indiya da Germany sun sanar da mahalarta toron yadda Kasashen su suke gudanar da Yansandan Jihohi ba tare da wata matsala ba kuma sunyi alkawarin bayar da shawarwari da tallafi wajen ganin  Najeriya ta aiwatar da tsarin ba tare da wata matsala ba.
Abun jira a gani shine Majalisar Taraiya za ta cigaba da tuntuba da tattauna da yin nazari akan hanyoyi da za su hana yin amfani da Yansandan don cimma buri na siyasa. Wanda da ga karshe sai Shugaban  Kasa ya amince da wadannan kudure kafin Dokar tayi aiki.
Taron ya sami halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Mataimakin Shugaban Majalisar Datttawa, Barau Jibrin da Sarakuanan Zazzau da na Ife da Ministoci da Shugabannin Diplomasiyya da ga kasashe daban daban da Kwararru akan harkar tsaro da Kungiyoyi ma su yawa da sauran Yan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here