Home Siyasa ‘Yan sanda na bincike kan harin da aka kai wa tawagar Peter...

‘Yan sanda na bincike kan harin da aka kai wa tawagar Peter Obi a Legas

184
0

A Najeriya, an kai wa magoya bayan jam’iyyar Labour hari yayin da suke halartar gangamin yaƙin neman zaɓe na ɗan takarar shugabancin ƙasa, Peter Obi.

‘Yan sanda sun ce suna bincike game da harin da aka kai a Jihar Legas, inda aka jikkata mutum huɗu kuma aka lalata motar da suke tafe a cikinta.

Mista Obi na fatan lashe zaɓen a matsayin ɗan takara na farko da ke gaba-gaba a wata jam’iyya, wadda ba waɗanda aka saba ba da su ba; wato PDP da kuma APC mai mulki a yanzu.

Yayin da ya rage saura mako biyu a fara kaɗa ƙuri’a, shi ne ke kan gaba a ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ta intanet, amma wasu na kokwanto game da ko zai iya samun ƙuri’u a zaɓen. BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here