Home Kwadago ’Yan Kwadago Sun Dakatar Da Zanga-Zanga Bayan Ganawa Da Tinubu

’Yan Kwadago Sun Dakatar Da Zanga-Zanga Bayan Ganawa Da Tinubu

204
0
NLC Shugabanni DA TINUBU

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun sanar da cewa za su tsagaita da zanga-zanga domin su ba gwamnati damar cika alkawuran da ta daukar wa ’yan Najeriya.

A ranar Laraba ce kungiyoyin a duk fadin Najeriya suka fantsama zanga-zanga don nuna bacin ransu game da janye tallafin man fetur da kuma wasu manufofin gwamnati da suka ce suna gallaza wa talakawa.

A kan haka ne Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gayyaci shugaban NLC, Joe Ajaero da na TUC, Festus Osifo, domin tattaunawa a Fadar Shugaban Kasa da yammacin Laraba.

Bayan kammala taron, Ajaero ya shaida wa ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa cewa bayan tattaunawar, sun amince su ba gwamnatin karin lokaci domin ganin kamun ludayinta.

A cewarsa, “Yana da muhimmanci mu sanar da ’yan Najeriya cewa babbar nasarar da zanga-zangarmu ta samu ita ce bukatar Shugaban Kasa, Bola Tinubu, ta tattaunawa da NLC da TUC a sirrance.

“Mun tattauna muhimman bayanai kan abubuwan da suka taso bayan janye tallafi. Mun tattauna muhimman batutuwa masu muhimmanci. Daga ciki ya tabbatar mana da cewa za a farfado da matatar man fetur ta Fatakwal kuma za ta fara aiki nan da watan Disamba.

“Ya kuma yi mana alkawarin cewa za a kara wa ma’aikata mafi karancin albashi nan ba da jimawa ba.

“Daga karshe, muna gode wa ’yan Najeriya yayin da za mu ci gaba da jiran gwamnati mu ga kamun ludayinta ta bangaren cika nata alkawarin, kamar yadda mai girma Shugaban Kasa ya amince,” in ji Shugaban na NLC. (Aminiya).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here