Home Tsaro ‘Yan fashin daji sun ƙone mutum 32 a gidajensu a Madagascar

‘Yan fashin daji sun ƙone mutum 32 a gidajensu a Madagascar

147
0

Hukumomi a Madagascar sun ce wani gungun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashin daji ne sun kashe mutum aƙalla 32 ta hanyar ƙone su a cikin gida.

‘Yan sanda sun ce an gwamutsa mutanen cikin gidaje biyu ne ranar Juma’a kuma aka cinna musu wuta. Mutum uku sun ji munanan rauni kuma suna samun kulawar gaggawa a asibiti.

Hotunan da aka yaɗa a intanet sun nuna ɓaraguzan ginin ne kawai suka rage bayan ƙona su a yankin Ankazobe da ke kusa da Antananarivo babban birnin ƙasar.

Rundunar sojan sama ta ƙasar na amfani da jiragen helikwafta wajen neman miyagun da suka ƙona maza da mata da yaran.

Ministan tsaro na ƙasar ya ce yana tunanin an kashe su ne saboda mutanen ƙauyen suna bai wa jami’an tsaro bayanai game da ‘yan fashin.

Jami’an tsaro sun ce wasu ‘yan fashin shanu ne suka aikata kisan waɗanda ake kira “daholo” a ƙasar.

Satar shanu da kuma yunƙurin daƙile ta sun haddasa mummunan rikici a bayan-bayan nan a Madagascar. (BBC Hausa)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here