Home Tsaro YAN DABA SUN KASHE MUTUM GUDA, SUN RAUNATA DA DAMA A KANO

YAN DABA SUN KASHE MUTUM GUDA, SUN RAUNATA DA DAMA A KANO

260
0
Yandaba
Yandaba

Fadan daba ba wani sabon abu bane a birnin Kano. A lokuta  da  dama ana samun gungun Yan daba dauke da muggan makamai wadanda suka hada da Barandami da Adda da Gariyo da Takobi da wukake da  sauransu suna afkawa mutane.

Su kanyi Kungiya ne, wani lokaci kamarsu su Dari ko Hamsin ko makamantan haka; su kuma dumfari wata unguwa ko kuma tituna  suna saran mutane suna kuma yi musu kwace na dukiyoyin su; musamman wayar hannu.

A  cikin wannan satin ne irin wadannan matasa; dauke da makamai suka shiga unguwar Yakasai, wacce akafi sani da Sabuwar Unguwa inda suka rinka saran mutane baji ba gani.

Binciken Jaridar Viewfinderng.com ya tabbatar da wannan al’amari a inda muka zanta da wasu da aka sara. Wani Al’majiri da aka sara yayin da yake karatu a kofar gidan da sukeyin karatun Allo ya sheka Lahira a Jiya Al’hamis bayan an kaishi Asibitin Kwararru na Murtala.

Wani Jami’i dake aiki a Asibitin ya tabbatar mana da rasuwar Almajirin bayan kwana daya da kaishi asibitin.

Malam Umar Hussaini wani mazauni a Unguwar Yakasai ya tabbatar mana da faruwar al’amarin. Yace an sari mutane da yawa. Akwai wanda aka farde masa baki da wuka, wasu kuma an yankesu a sassa daban-daban na jikinsu.

Wani mai sana’ar waya a Sabuwar Kasuwar waya mai suna  Bashir yace, an fasa shagunan waya da dama kuma an kwashe musu wayoyi.

Jaridar Viewfinderng.com, ta gano cewa lamarin ya farune bayan Sallar Isha’I na ranar Laraba kuma ana zargin wasu da  ake zaton magoya bayan wani dan siyasa ne suka je unguwar domin neman fansar dan uwansu da aka sara a lokacin da  akayi zaben fidda gwani na Jam’iyar APC a filin wasa na Kofar Mata yan kwanankin baya.

Majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa zafin kaye da gwanin nasu yasha da kuma saran da akayiwa dan uwannasu ne yasa sukaci alwashin daukar fansa kuma shine dalilin nasu na yin wannan aika aika.

Malam Habibu, Mai Ungugawar Yakasai “B” ya tabbatarwa da Jaridar Viewfinderng.com faruwar wannan al’amari. Tare da tabbatar da rasuwar daya daga cikin wadanda aka sara.

Sai dai yace, wadanda suka aikata wannan al’amari wasu yara ne guda uku yayan wani Malami da ake kira Malam Bature sune, suka gaiyato abokansu suka rinka saran mutane suna kwace musu wayoyin hannu.

Mai Unguwa Habibu yace, Yankwamitin Unguwarsa sun sami nasarar kama daya daga cikin Yaran kuma ya basu umarni dasu mika shi ga hukumar Yansanda dake Kwalli kuma tuni sunyi hakan.

Ya kara da cewa, ya bawa Yankwamitin umarnin dasu saka ido da zarar sunga wadannan Yara su biyu da suka gudu da su damkesu su mikawa hukumar Yansanda.

Kokarinmu na samun Kakakin Rundunar Yansanda na Jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa don muji bahasinsu yaci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here