Home Labaru masu ratsa Zuciya ‘Yan bindiga Sun Sace Gomman Mutane A Zamfara, Katsina, Kashe ’Yan Gudun...

‘Yan bindiga Sun Sace Gomman Mutane A Zamfara, Katsina, Kashe ’Yan Gudun Hijira 34 A Binuwai

181
0

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ‘yan fashin daji sun yi garkuwa da mutane da dama a wasu yankuna da suka hada iyaka da jihohin Zamfara da Katsina.

Bayanai sun yi nuni da cewa lamarin ya faru ne a Kucheri, Wanzami da Danwuri da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Sai kuma mutanen da aka sace a garin ‘Yankara da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Jihohin biyu da ke makwabtaka da juna na arewa maso yammacin Najeriya ne.

Gidan talbijin na Channels ya ce mutum kusan 60 aka kwashe a yankunan.

Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a a lokacin da ‘yan fashin dajin ke fitowa daga dajin Sabubu da ke Zamfara zuwa dajin Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna

Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa ‘yan bindigar na tserewa harin dakarun Najeriya ne a lokacin da aka gan su suna kaurar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar da yawa daga cikinsu.

Shaidu sun ce yayin da suke tserewa ne ‘yan fashin dajin suka rika daukar mutanen da suka tarar a yankunan da suke ratsawa, wadanda bayanai suka yi nuni da cewa mafi yawansu yara ne kanana.

Jaridar Daily Trust ta ce akalla mutum 100 ‘yan bindigar suka sace a gonaki a tsakanin jihohin na Zamfara da Katsina bayan da suka abkawa yankunan.

Yaran da aka sace sun je yi itace ne a daji yayin da manya kuma sune je gonakinsu ne.

Hukumomin tsaro bas u ce komai dangane da lamarin ba, amma shaidu da dama a yankunan sun tabbatar da aukuwar lamarin.

“Wasu daga cikin iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su sun yi kokarin neman manya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, amma ba su same sub a.” Wani shaida ya fadawa jaidar Trust.

Satar mutane domin neman kudin fansa ta ragu a ‘yan watanni baya, amma a ‘ya n kwanakin nan matsalar na kara kunno kai.

Dadin da dawa wasu ’yan ta’adda sun kashe akalla mutum 34 a wani sansanin ’yan gudun hijira da ke wata makarantar firamaren gwamnati a Karamar Hukumar Guma ta Jihar Binuwai.

Mai ba da shawara kan sha’anin tsaro na karamar hukumar, Christopher Waku, ya shaida wa Aminiya cewa wasu mutum sama da 40 kuma sun samu raunuka a harin da aka kai da misalin karfe 9 na dare ranar Juma’a.

Da yake bayani kan abin da ya gani a wurin, Waku ya ce, “Mun gano gawarwaki 24 a cikin wani aji, da wasu 10 kuma a kan hanyar kauyen; su kuma an kashe su ne a yayin da suke kokarin tserewa.”

Kakakin ’yan sanda ta Jihar Binuwai, Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin rubutaccen sakon da ta tura wakiliyarmu cewa, “tabbas hakan ta faru.”

Wani shaida mai suna John ya bayyana mana cewa wata mata mai juna biyu da danta suna daga cikin ’yan gudun hijirar da ’yan ta’addan suka hallaka a harin.

Ya ce an kai harin ne a matsugunin ’yan gudun jiharar da ke makarantar firamaren da ke unguwar Mgban da ke yankin Nyiev a Karamar Hukumar Guma.

Ko a ranar Alhamis, Aminiya ta kawo rahoton kisan wasu mutum 46 da wasu ’yan bindiga suka yi a Karamar Hukumar Otukpo ta jihar ta Binuwai.

Mutanen da aka kashe, ciki har da iyalan shugaban karamar hukumar, Bako Eje, sun gamu da ajalinsu ne a yayin da ake zaman makokin wasu mutum uku da wasu mahara suka kashe kafin ranar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here