Home Siyasa Yan Adawa Ku Rungumi Kaddara, Ku Zo Mu Gina Mazabar Ikara/Kubau –...

Yan Adawa Ku Rungumi Kaddara, Ku Zo Mu Gina Mazabar Ikara/Kubau – Inji Hon. Damau

304
0
Hon. Damau Ikara

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Ikara/ Kubau , Aliyu Mustapha Abdullahi , Yariman Damau ya yi kira da Yan adawa daga mazabarsa da su rungumi kaddara kuma su zo su hada gwiwa  da shi domin kawo cigaba mai dorewa a mazabarsa.

Hon. Damau ya yi wannan kira ne bayan da ya samu nasara a karo na biyu a Kotu inda ya ce ya kamata abokin hamaryar sa ya fahimta cewa Allah ne ya ke bayar da mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so.

“ Ya kamata mutane su gane cewa Allah ne ya ke bayar da mulki ga wanda ya so, a kuma lokacin da ya so. Kafin abokin takarata ya zo wannan mukami malisa wani ne a wurin, yanzu kuma Allah ni ya bawa nasara har sau biyu; kuma nima ba zan dauwama akan kujerar ba , dole na sauka na bawa wani”.

Dan Majalisar ya godewa Allah da ya bashi wannan nasara kuma ya yi kira ga wanda ya kayar da sauran wadanda su ka taba zuwa wannan mukami a baya da su zo su hada karfi da karfe don gina mazabar Ikara da Kubau domin cigaban al’umar su.

Hon. Damau ya kara da cewa burinsa shine ya ga ya kawo cigaba zuwa mazabarsa sabo da haka yana bukatar shawarwari daga yan siyasa da sauran mutanen gari wajen ganin an bunkasa yankin.

Har ila yau dan Majalisar ya yi alkawarin ganin cewa ya karfafawa matasa da mata gwiwa da suke wannan yankin musamman ta bangaren neman ilimi da kuma samar da sana’o’I da za su kawo wa yankin cigaba.

Hon. Damau ya yabawa Hukumar zabe da Kotunan zabe wadanda suka jajirce wajen ganin gaskiya ta yi halinta. In da ya ce wannan nasara da ya samu kotun sauraron koke-koken zabe da kutun daukaka kara ya nuna karara irin soyayyar da mutanen yankisa sukeyi masa.

Sabo da haka Hon. Damau ya yi alkawarin ganin cewa bazai bawa mutanen mazabarsa ta Ikara da Kubau kunya ba a Majalisar Taraiya. Inda ya kara da cewa zai yi duk iyakacin kokarin sa wajen ganin ya kawo mu su romon demokradiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here