Home Uncategorized Yaki Da Ta’addanci: Majlisar Wakilai Ta Roki Shugaban Kasa...

Yaki Da Ta’addanci: Majlisar Wakilai Ta Roki Shugaban Kasa Da A Canza Salo

139
0
IMG 20240605 WA0059

Majalisar Wakilai ta roki shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya zauna da shugabannin Tsaro da Gwamnoni don sabunta salon yaki da ta’aaddaci wanda yaki ci ya ki cinyewa musamman a yankin arewacin Kasarnan.

 

Majalisar ta gabatar da wannan bukata a sakamakon wani kuduri da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Jibiya da Kaita ya gabatar tare da hadin gwiwar duka mambobin Jihar Katsaina da na wasu Jihohin ma su ka gabatar a zauren Majalisar jiya Laraba.

 

Dan Majalisa Sada Soli ya yiwa Yan Jaridu Karin haske game da kudurin in day a ce dalilin sun a dunkulewa don gabatar da kudurin shine sun  lura da cewa matakai da ake dauka sunki yin wani tasiri  da ake bukata shi ya sa suka nemi Majalisar da ta roki shugaban Kasa Bola Tinubu daya sa ke zama da jami’an Tsaro don sake fito da wani sabon salon a yaki da ta’addanci a jihohi guda shida dake  Arewa maso Yamma.

 

Hon. Soli ya kara da cewa har ila yau sun roki shugaban Kasar da ya zauna da Gwamnoni domin sake tattaunawa da su wajen fito da sabuwar hanyar tun da sune shugabannin Tsaro a Jihohin na su.

 

Dan Majalisar y ace sun roki gwamnonin das u yi watsi da batum yin sulhu da Yan’ta’addan sabo da sun a da shugabanci daban-daban wanda yana da wahala a iya yin sulhu da dukkan kungiyoyin.

IMG 20240605 WA0084

Hon. Abubakar Yahaya Kusada Dan Majalisar Wakilai mai Wakiltar Kankia Kusada da Ingawa da ga Jihar Katsina ya nuna goyan bayan sa akan wannan kuduri in da ya ce matsalar Tsaro tafi damun Al’ummar Jihar Katsina.

 

Ya ce wannan matsala tana bukatar sabon salo sabo da yadda ake yakar Yan ta’addan baya aiki domin   koda yaushe ana jiransu ne sai sun kawo hari kafin a yake su. Ya ce a maimakon haka ya kamata a rinka kai musu hari maimakon a rinka jiran su.

 

Hon. Kusada ya kara da cewa mutanen Jihar suna fuskatar cin zarafi iri-iri wanda ya hada da kisa da nakasa da fyade da sauran su sabo da haka akwai bukatar ayi duk mai yiwuwa wajen ganin an kawo karshen matsalar ta kowanne hali.

 

Kusada ya amince da cewa su kansu Yan Majalisar basa yin aikin su kamar yadda ya kamata wajen bibiya kamar yadda Dokar Kasa ta basu dama amma y ace sunayi gwargwadon iyawa.

 

Dagtsatsaa karshe ya roki sojojin da sauran jami’an Tsaro das u saka kishin Kasa wajen gudanar da aikin su in da kumloa ya roki Shugabannin Jami’an Tsaro das u tabbata suna bawa kananan jami’ancjankasba  hakkokin sun a alawus-alawkuduri niyyar us wanda hakan zai kara musu Karin gwiwa.

IMG 20240605 WA0080

A wani bangare kuma Yan Majalisar Wakilai dag a Jam’iyar APC daga Yankin Arewa   Yamma sunyi wani taro na musamman wanda mataimakin Shugaban Kungiyar Hon. Aminu Jaji ya ce dalilin taron shine don a tattauna matsalolin yankin.

 

Ya ce batum ta shikne ya fi Jan hankalin Yan Majalisar kuma sun kuduauri niyyar yin duk mai yiwu wa wajen ganin aaran kaawo karshen matsalar tsaro a yankin ta hanyar ganawa da Shugaban Kasa da sauran ma su ruwa da tsaki.

Bayan haka ya ce sun tattauna akan batum karasa hanya Abuja zuwa Kaduna da kuma Katsina zuwa Sokoto wadanda su ka ce su na da mutukar muhimmanci ga al”umar yankin dama Najeriya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here