Home Mai da Iskar Gas Yajin Aiki: Tinubu Zai Kafa Kwamiti Don Duba Bukatun NLC

Yajin Aiki: Tinubu Zai Kafa Kwamiti Don Duba Bukatun NLC

182
0

Gwammnatin Najeriya, za ta kafa wani kwamiti da zai duba bukatun da kungiyar kwadago ta NLC ta gabatar mata.

Kakakin gwamnatin tarayya Dele Alake ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan da aka kammala wani zama tsakanin wakilan gwamnati da na kungiyar ‘yan kasuwa ta TUC wacce mamba ce a kungiyar ta NLC.

Gamayyar kungiyar kwadagon ta Najeriya ta tsara shiga yajin aiki a ranar Laraba don kalubalantar karin farashin litar mai.

Kungiyar kwadgon ta ce tana neman gwamnati ta maido da farashin litar mai yadda yake a baya.

Sai dai yayin da wa’adin shiga yajin aiki ke karatowa, bangarorin biyu na ta tattaunawa don neman maslaha, inda har kungiyar ta kwadago ta gabatar da wasu bukatu kafin ta janye yajin aikin da take shirin shiga.

Daga cikin bukatun da kungiyar ta NLC ta gabatar, akwai neman a kara mafi karancin albashi ga ma’aikata.

Alake yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadi ya ce gwamnati za ta duba bukatun kungiyar.

Ya kara da cewa Shugaba Bola Tinubu zai kafa wani kwamitin da zai hado wakilan gwamnati, da na kungiyar kwadago da kuma na bangaren kamfanoni ko ‘yan kasuwa masu zaman kansu.

A ranar 29 ga watan Mayu, Tinubu ya karbi mulki a hannun tsohon shuba Muhammadu Buhari.

A ranar Talata ake sa ran bangarorin biyu za su sake zama don ci gaba da tattaunawa.

Farashin litar mai ya tashi daga naira 185 zuwa 350 a wasu wurare ma har 550 a Najeriya, tun bayan da Shugaba Tinubu ya bayyana cire tallafin man a jawabinsa na farko. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here