Home Labaru masu ratsa Zuciya Yadda ‘Yan Ta’adda Su Ka Yi Wa Manoma 8 Yankan Rago A...

Yadda ‘Yan Ta’adda Su Ka Yi Wa Manoma 8 Yankan Rago A Borno

257
0
Farmers Killed in Borno

A ranar Jumma’a jami’ai sun baiyana cewa ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin Najeriya sun yi kisan gilla ga manoma takwas, tare da sace wasu 10.

Wannan shi ne sabon hari da ‘yan ta’addan su ka kai a yankin da ke yanayin zullumi, inda kazalika miyagun irin su ke barazanar katse hanyar samar da abinci.

A ranar alhamis ne akasin ya auku a yankin Mafa, inda ‘yan ta’addan su ka yi wa manoman kwantan bauna da yi mu su yankan rago.

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ce harin na da zummar mayar da hannun agogon nasara kan ta’addanci ne baya, yayin da gwamnati ke fafutukar mayar da dubban wadanda su ka rasa muhallan su gida da sama mu su sabuwar rayuwa.

Ya ce akwai bukatar jami’an tsaro su kara himmar tunkarar kalubalen yayin da su ma jama’a ya dace su dau matakan kauda bara.

“Lalle mu tsaya kan dugadugan mu don magance matsalar” Inji Zulum da ya kara da cewa ya umurci jama’a su rika yin ta maza su kuma rika lura da abubuwan da ka iya tarnaki ga tsaro su kuma kaucewa zama a ihun ka banza.

‘Yan ta’addan sun kaddamar da yakin bijirewa hukumomi a 2009 da muradun kafa daular su ta shari’ar mudulunci bisa fahimtar Boko Haram.

Akalla an yi kisan gilla ga mutum dubu 35 inda a ka raba fiye da mutum miliyan 2 da gidajen su daga hare-haren Boko Haram da kuma bangaren da ke da mubaya’a ga ‘yan I.S ko DAESH.

Manoma a Borno sun sha fuskantar hare-hare a ‘yan watannin nan da hakan ke kawo fargabar yunwa mai tsanani inda hukumomin majalisar dinkin duniya ke gargadin samun karancin abinci.

A jiya Jumma’a manoman sun shiga juyayin ‘yan uwan su da a ka yi wa kisan gilla da kuma kokawa ga karancin matakan tsaro a dazuka da sassa masu hatsari. (Muryar Amurka).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here