Home Cinikaiyar Zamani Yadda Wa’adin Ecowas ga Nijar ya tsunduma arewacin Najeriya cikin fargaba

Yadda Wa’adin Ecowas ga Nijar ya tsunduma arewacin Najeriya cikin fargaba

172
0
Map Niger Nigeria

Ana cike fargaba da zaman ɗar-ɗar bayan cikar wa’adin da Ecowas ta bai wa sojojin Nijar, na su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum ko kuma su fuskanci yiwuwar ɗaukar matakin sojoji daga ƙungiyar ƙasashen.

Ranar waccan Lahadin ce, shugabannin Ƙasashen Afirka ta Yamma suka bai wa masu juyin mulkin wa’adin mako ɗaya a kan su yi biyayya ga buƙatunsu ko kuma su “ɗauki dukkan matakai… [waɗanda] suna iya haɗar da amfani da ƙarfi”.

Sai dai a maƙwabciyar Nijar, Najeriya – inda da yiwuwa sojojin da za a tura Nijar masu yawa za su fito – amon masu nuna adawa da ɗaukar matakin soji yana daɗa ƙarfi.

Ƙasashen biyu kuma suna da alaƙa ta kusancin al’umma da kuma tarihi.

Ranar Asabar, majalisar dattijan Najeriya ta buƙaci gwamnati ta nemi “zaɓin siyasa da na diflomasiyya”, wajen shawo kan wannan dambarwa.

A birnin Sokoto da ke arewacin Najeriya, mai iyaka da Jamhuriyar Nijar, inda sansanin Runduna ta 8 ta sojojin Najeriya take, fargaba tana ƙaruwa.

Sansaninta yana kan wata babbar mahaɗa a kan titin da ya nufi Nijar kuma mai yiwuwa wurin ya zama cibiyar tattara dakarun soji, kafin ɗaukar duk wani matakin amfani da ƙarfi.

Kwanciyar hankali da lumanar da ta lulluɓe unguwannin Sokoto sun sakaya ƙaruwar tunzurin da birnin har ma da sauran sassan jihar ta arewa maso yamma suka shiga.

Wani al’amari da ya janyo haka shi ne – a cewar mazaunan birnin – duk ɗaya cikin mutum biyar da ke Sokoto daga Nijar ko kuma suna da alaƙa da ƙasar.

Makekiyar unguwar Sabon-Gari Girafshi da ke wajen birnin na Sokoto mafi yawa tana karɓar baƙuncin mutane ne daga Nijar. Suna fargabar cewa tura sojojin da Ecowas ke hanƙoron yi na iya shafar danginsu sosai har ma zai iya illa ga tsaron rayukansu su da ke nan Najeriya.

Wani magidanci ɗan shekara 51 da ke sana’ar kayan yari, Sulaiman Ibrahim yana zaune a ɗaya daga cikin gidajen da zagaye da katanga, ga kuma ƙatuwar ƙofa.

Ɗaya daga cikin matansa da wasu ‘ya’yan nasa suna Yamai, babban birnin Nijar, an ritsa da su a can saboda juyin mulkin ƙarshen watan jiya.

“Yanzu ina son na kira mai ɗakina Fatima don ji halin da suke ciki, saboda tun ranar da aka yi juyin mulkin, ban iya magana da ita ba,” ya faɗa wa BBC, riƙe da wayarsa a hannun hagu.

Yana bincikawa ƙasa cikin sunayen mutanen da yake tuntuɓa kuma ya sake buga wa matarsa waya.

Duk kiran da ya yi, saƙo iri ɗaya yake samu: “Lambar da kake kira, ba a samun ta a wannan lokaci.”

“Duk lokacin da na yi kira, abin da suke faɗa min kenan, ko ba sabis ne ko kuma wata matsalar ce, ban sani ba,” ya faɗa cikin ɓacin rai, kuma ya kasa ɓoye damuwar da yake ciki.

“Idan sai an yi amfani da ƙarfin soji a kan Nijar, wannan zai janyo ƙarin tashin hankali. Ina cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi saboda iyalina ba sa tare da ni, kuma ba ni da wani labari game da su.”

Ya buɗe manhajar hoto a wayarsa don ganin ɗansa mai shekara 18 da wani ɗan’uwansa kuma.

“Wannan ɗana ne Mustapha, yanzu haka yana Nijar. Wannan kuma ƙaninsa ne, shekararsa shida, duka suna tare da mahaifiyarsu.”

Ba Sulaiman kaɗai ba ne a irin wannan hali.

Kullum yana gamuwa da sauran maƙwabtansa daga Nijar don jin ko wani a cikinsu ya samu labarin gida.

Mohamadu Ousman mai shekara 43, ya nanata ra’ayin mutane masu yawa da ke nan cewa amfani da ƙarfi don mayar da hamɓararren shugaban ƙasar kan mulki na iya janyo wata masifar.

“Ga Ecowas ta auka wa Nijar da yunƙurin ƙwatar mulki daga sojoji don mayar wa fararen hula, ba ma fatan haka, Allah ya kiyaye. Tamkar rusa tarihinmu ne,” ya bayyana wa BBC.

Zainab Saidu, mai shekara 59, ta fito ne daga birnin Dosso na jamhuriyar Nijar, amma yanzu tana zaune ne akasari a Sokoto bayan ta auri wani ɗan Najeriya. Ɗan’autanta yanzu haka yana can Nijar kuma tana fargaba game da tsaron rayuwarsa.

“Na damu. Na rantse dukkanmu muna cikin fargaba, duk wanda ya fito daga Nijar. Kowa ya kaɗu sosai musamman lokacin da muka ji cewa Najeriya za ta iya shiga Nijar da niyyar yaƙi, ” ta ce.

A ranar Juma’a, manyan hafsoshin tsaro na Ƙasashen Afirka ta Yamma suka ce sun amince da wani shiri na yiwuwar tura sojoji, amma Ecowas na ci gaba da bin matakan diflomasiyya don lalubo mafita.

A wani ƙoƙarin ƙara matsa lamba, ƙungiyar ƙasashen yankin ta kuma ƙaƙaba takunkumai a kan shugabannin juyin mulkin sannan ta rufe kan iyakoki da Nijar. Bugu da ƙari, Najeriya ta yanke wutar lantarkin da take bai wa arewacin ƙasar.

Sai dai, hakan na nufin su ma mutanen da ke cikin iyakar Najeriya, lamarin ya shafe su.

Ɗaya daga cikin garuruwan kan iyaka da ke jin raɗaɗin wannan lamari, shi ne Illela mai nisan kimanin kilomita 135 daga birnin Sokoto.

Cibiyar hada-hadar kasuwanci ne, amma yanzu idan an gan shi, yadda ka san wani gari da ke cikin matsi da takurar tattalin arziƙi.

A mashigin gari, ga dogon layin ababen hawa nan da suka rasa abin yi, akasari manyan motoci ne da lodin kaya lulluɓe da tamfol don kare su daga ruwan sama da rana.

Direbobi kuma sun taru a inuwar manyan motocin ko dai suna barci ko kuma suna zaune da wayoyin salularsu ko kuma rediyo, suna jiran su ji labarai game da ci gaba na baya-bayan nan da aka samu game da batun kan iyaka.

Wani direban babbar mota, Abdullahi, sanye da tishat da koɗaɗɗen shuɗin wando, yana riƙe da ledar ruwa.

Yan Niger Nigeria

“Na maƙale a nan tsawon kwana uku yanzu,” ya ce.

“Duk kuɗin da ke jikina sun ƙare. Aljihuna babu ko ƙarfamfana. Abokina ne ya saya min abinci da safiyar nan. Shi ya sa kuka gan ni riƙe da ledar ruwa. Ina ta kiran ubangidana don yi masa bayani game da halin da nake ciki kuma na sanar da shi cewa rufe kan iyaka ya ritsa da ni, amma ba ya amsa kiraye-kirayena.”

Abokan aikin da ganinsu duk sun gaji, wasu kuma saddaƙar.

Suna iya fuskantar jira na tsawon lokaci kuma kayan da suka ɗauko yana iya lalacewa, abin da zai haddasawa ‘yan kasuwa masu kayan ɗumbin asarar kuɗi.

Sauran waɗanda lamarin ya yi matuƙar nakasa harkokin kasuwancinsu, akwai Ado GWani magidanci ɗan shekara 42, sau da yawa yakan je Nijar ya sayo ƙanƙarar da zai sayar wa ‘yan kasuwa masu harkar ruwa da lemon kwalba, da ke buƙatar sanyi a Illela.

Sai dai harkar Ado Garba ta yi matuƙar durƙushewa saboda ba ya iya zuwa Nijar ya saro ƙanƙara yanzu.

“Nakan yi naira 100,000 a rana da kayan da nake sarowa. Amma yanzu, ba zan iya tsallaka kan iyaka ba. Akwai sojoji da ‘yan sanda da jami’an hana fasa-ƙwauri da da jami’an shigi da fice an girke su a ko’ina. Idan ka tsallaka iyaka, komai ya faru, ruwanka,” mai sayar da ƙanƙarar ya ce.

Jami’an hana fasa-ƙwauri sun gana da wasu daga cikin ‘yan kasuwar Illela a ranar Juma’a a ƙoƙarinsu na shawo kan damuwar da suke da ita da kuma yi bayani kan abin da ya wajabta rufe kan iyakar.

“Babu sadaukarwar da ta fi buƙatar tabbatar da zaman lafiya da kuma mulkin dimokraɗiyya a cikin wannan yanki. Al’umma ta fahimci dalilin da ya sa aka rufe kan iyakar,” in ji Bashir Adewale Adeniyi daga hukumar hana fasa-ƙwauri.

Sai dai haƙurin mutane a Illela da sauran wurare a Sokoto yana ƙurewa – zuwa yanzu kuma, ƙanƙanuwar alama ake iya gani, da ke nuna ko shugabannin juyin mulki a Nijar za su ja da baya.

arba Dankwaseri. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here