Home Tsaro Yadda Sojoji Suka Ceto Sama Da Mutum 60 Daga Yan Bindiga A...

Yadda Sojoji Suka Ceto Sama Da Mutum 60 Daga Yan Bindiga A Jihar Zamfara

234
0
Sojoji Ceto

Rundunar sojin Najeriya bataliya ta 223 karkashin rundunar Hadarin Daji da ke fada da ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto sama da mutum 60 a farmakin da ta kaddamar kan ‘yan fashin daji daga jihar Kebbi zuwa Zamfara a cikin kwana tara.

Sun hada da mutum 24 da aka ceto yayin wata arangama da yan bindigar a yankin Maru na jihar Zamfara.

Kwamandan rundunar ta Hadarin Daji a jihar Zamfara Birgediya S Ahmed, ya shaida wa BBC cewa suna kokarin kakkabe yan bindigar ne domin ba manoma damar noma abin da za su ci yayin da damuna ta kankama.

Ya ce an faro aikin ne tun daga jihar Kebbi da ke makwabtaka aka dangana har zuwa jihar Zamfara inda aka tike.

Ya ce a wani gari da ake kira Kabugu Lamba, da ke karamar hukumar Maru ne mayakansu suka samu nasarar ceto mutum 24 daga hannun ‘yan bindigar, bayan kwashe wani lokaci a hannun masu garkuwa da su.

A cewarsa: ” Tun da muka fara wannan aiki tara da suka wuce, mun kwato fiye da mutane 63.”

Ya kara da cewa suna ci gaba da kokari ne duba da yadda damina ke kankama, don haka akwai bukatar a bai wa mutane damar komawa gona domin noma abincin da za su ci.

Ya ce ko a ranar Lahadi sun kwato mutum 12 a yankin karamar hukumar Shinkafi, aka sake kwato mutum bakwai, a wajen garuruwan Kware da Dutsi.

Ya ce sai dai babban kalubalen da suke fuskanta a wannan fada da ‘yan fashin daji shi ne yadda wasu ke ba su bayanan sirri, abun da ke ba su damar sanin duk wani motsi da sojojin suka yi.

”Ko da yake mun gane cewa akwai wadanda ake tursasawa bayar da bayanai ta hanyar yi musu barazana, amma akwai zauna gari da ake biya domin kawai su yi hakan”.

Kwamandan ya ce za su ci gaba da zage dantse domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali sun samu, domin jama’a su samu damar rayuwa cikin salama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here