Home Siyasa Yadda Sanata Akpabio/ Barau Suka Zama Shugabannin Majalisar Datttawa Ta Goma

Yadda Sanata Akpabio/ Barau Suka Zama Shugabannin Majalisar Datttawa Ta Goma

250
0

Godwills Akpabio ne ya samu nasara a zaben Majalisar Datttawa da kuri’u 63 inda abokin hamaiyar  sa Abdulaziz Yari ya sami kuri’a 46, a in da daya da ga cikin sanatocin bai zabi kowa ba.

 

Ba tare da bata lokaci ba Akawun Majalisar Sani Magaji Tambawal ya rantsar da Akpabio a Matsayin Shugaban Majalisa ta goma.

Bayan an rantsar da Sanata Akphabio; take aka gabatar da bukatar Sanata Barau Jibrin day a zama mataimakin sa. Take aka  Sanata Barau ya amince day a zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

 

Akawun Majalisar Dattawa Sani Magaji Tambawal ya gabatar da bukatar ga Yan Majalisar kuma ya nemi ko akwai wani da shima yake da bikata ta ya zama Mataimakin Shugaban. Babu wanda ya kalubalanci takarar Sanata Barau Jibrin.

 

Akawun Majalisar yace tunda ba wanda ya kalubalanci takarar Sanata Barau na zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa hakan ya nuna cewa Sanata Barau ya zama Mataimakin Shugaba ta Majalisar ta goma.

Zaben ya gudana cikin tsarist ba tare da wata hatsaniya ba.

 

Tun da farko Yan Majalisar Datttawa mutum biyu ne suka nuna shaawar su na shugabancin Majalisar. Sune Sanata Godwills Akpabio da Sanata Abdulaziz Yari.

 

Sanata Ali Ndume ne ya gabatar da takarar Akpabio in da Sanata Abbo ya gabatar da takarar Sanata Abdulaziz Yari na Shugabancin ta Majalisa ta 10.

 

Bayan sun amince da gabatar da takarar su Akawun Majalisar Dattawa Sani Magaji Tambawal na Majalisar ne ya nemi ko akwai Karin mai sha’awar  takara ba a samu ba sai ya bayar da umarnin da a fara zabe da da misalin 8: 30 na safe.

 

Zaben ya cigaba da gudana a cikin tsari da ga A zuwa Z in da Jihohi da suka fara da harafin.

 

Bayan an kammala zaben da misalin 9 : 12 na safe ba a bata lokaci ba aka fara kirga kari’a. Zabe ya kammala da misalign 9:30 amma an cigaba da zaben sauran mukamai na shugabancin Majalisar.

 

A Majalisar Wakilai ma zaben yana cigaba da gudana kamar yadda yake gudana a Majalisar Dattawa. Amma rahotanni na nuna wa cewa Tajuddeen Abas shi ke kan ga ba a kuri’a a yayin da zaben yak e cigaba da gudana a halin yanzu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here