Home Uncategorized Yadda Nada Shugabancin Majalisun Taraiya Ya Haifar Da Rikici A Jam’iyar APC

Yadda Nada Shugabancin Majalisun Taraiya Ya Haifar Da Rikici A Jam’iyar APC

197
0
APC National Chairman

Duk da cewa Majalisar Dokokin Najeriya ta bayyana sunayen Shugabanninta ranar Talata amma Shugaban Jam’iyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya ce Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyar na Kasa ya nisaanta kansa da ga nada wadannan Shugabanni.

Sanata Adamu wanda ya shugabanci taron da aka gudanar na Jam’iyar ranar 8 ga watan Mayu ya barranta Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyar APC da nadin Shugabancin Majalisar.

A wani bangaren kuma Sakataren Yada Labarai na Jam’iyar APC na Kasa, Felix Morka ya sanar cewa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ne ya amince da raba mukamai da akayi a Majalisar Taraiya zuwa shiyya – shiya kuma an amince da wannan ne a ranar taron 8 ga watan Mayu.

Tsohon Sanata Shehu Sani ya zargi Shuagabancin Majalisar Taraiya da yin watsi da uwar Jam’iyar APC wajen fidda Shugabancin Majalisun wanda yace hakan ya sabawa Kuddin Tsarin Jam’iyar ta APC.

Koma dai me ne ne Shugabannin Majalisun Taraiyar guda biyu wato Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ta Wakilai Dr. Tajuddeen Abbas sun sanar da Shugabancin Majalisun.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya sanar da Opeyemi Bamidele a matsayin, shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai.

Ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar na ranar Talata, inda ya bayyana Sanata David Umahi a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye.

Haka zalika ya ce rukunin ‘yan majalisar dattijai na jam’iyyar APC mai mulki sun amince da Mohammed Ali Ndume, a matsayin mai tsawatarwa na ɓangaren masu rinjaye a majalisar.

Sai kuma Sanata Oyelola Yisa Ashiru matsayin mataimakin mai tsawatarwa na ɓangaren masu rinjaye.

Jim kaɗan kuma haka ne, sai aka sanar da Sanata Simon Mwadkon Davou a matsayin shugaban marasa rinjaye, yayin da Oyewumi Olalere ya kasance mataimakin shugaban marasa rinjaye.

Haka zalika, an zaɓi Sanata Darlington Nwokocha, a muƙamin mai tsawatarwa na ɓangaren marasa rinjaye, sai Sanata Rufa’i Sani Hanga, mataimakin mai tsawatarwa na ɓangaren marasa rinjaye a majalisar dattijai.

A nasa bangaren Kakakin majalisar Wakilai  Dr. Tajuddeen Abbas ya ce manyan jami’an da za aka nada daga  jam’iyya Mai rinjaye sun sami goyan baya daga ‘yan majalisu 143 na Jam’iyyar APC.

Wannan a cewarsa ya hada da Farfesa Julius Ihonvbere daga jihar Edo a matsayin shugaban masu rinjaye, da Mista Halims Abdullahi daga jihar Kogi a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye, sai Usman Bello-Kumo daga jihar Gombe a matsayin babban mai tsawatarwa da Mrs Onanuga Adewumi daga jihar Ogun a matsayin mataimakiyar bulaliyar majalisa.

Ga shugabannin marasa rinjaye kuwa , kakakin majalisar ya bayyana Mista Kingsley Chinda na PDP daga jihar Rivers a matsayin shugaban marasa rinjaye, Ali Isa daga jihar Gombe na PDP a matsayin Mai tsawatarwa na marasa rinjaye, yayin da Aliyu Sani Madaki na NNPP daga jihar Kano ya kasance a matsayin mataimakin Shugaban marasa rinjaye, sai  Mista Ozidonabi George daga jihar Anambra na Jam’iyya LP a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.

Kakakin majalisar wanda ya taya su murna, ya yi addu’ar Allah ya ba su hikimar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A zantawarsa da mamema labarai jim kadan bayan kammamala zaman Majalisar, Dan majalisa Muhammad Danjuma Hassan na Jam’iyya NNPP daga Jihar Kano, duk da cewa ya fito daga bangaren marasa riinjaye ya bayyana gamsuwarsa da yadda rabon mukamin jagororin ya kasance.

Ya ce anyi adalci wajen raba mukamai domin anyi la’akari da irin gudunmawa da kowace jam’iya ta bayar da kuma yawan mambobi na kowacce jam’iya wajen raba mukaman.

Honarabul Hassan ya na da kyakkyawan fatan cewa wannan shugabanci na Majalisar zai gudanar da aiyuka wadanda zasu kawo cigaba a kasarnan.

Shugabannin Majalisar Dattawan Najeriya da in da su ka fito

Akpabio 2

 • Sanata Opeyemi Bamidele – Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Ekiti (kudu maso yamma)
 • Sanata David Umahi – Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Ebonyi (kudu maso gabas)
 • Sanata Ali Ndume – Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Borno (arewa maso gabas)
 • Sanata Lola Ashiru – Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Kwara (arewa ta tsakiya)

Yankunan da na marasa rinjaye suka fito:

 • Sanata Simon Davou na PDP – Shugaban Marasa Rinjaye daga Jihar Filato (arewa ta tsakiya)
 • Sanata Oyewunmi Olarere na PDP – Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye daga Jihar Osun (kudu maso yamma)
 • Sanata Darlington Nwokeocha na LP – Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye daga Jihar Abiya (kudu maso gabas)
 • Sanata Rufai Sani Hanga na NNPP – Mataimakin Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye daga Jihar Kano (arewa maso yamma)

Shugabannin Majalisar Wakilan Najeriya da yankunan su

Speaker Tajuddeen Abas

Masu rinjaye:

 • Julius Ihonvbere: Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Edo (kudu maso kudu)
 • Halims Abdullahi : Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Kogi (arewa ta tsakiya)
 • Bello Kumo: Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Gombe (arewa maso gabas)
 • Adewunmi Onanuga: Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Ogun (kudu maso yamma)

Marasa rinjaye:

 • Kingsley Chinda: Shugaban Marasa Rinjaye (PDP) daga Jihar Ribas a (kudu maso kudu)
 • Aliyu Madaki: Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye (NNPP) daga Jihar Kano a arewa maso yamma
 • Ali Isah: Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye (PDP) daga Jihar Gombe a arewa maso gabas
 • George Ozodinobi: Mataimakin Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye (LP) daga Jihar Anambra a kudu maso gabas

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here