Home Siyasa Yadda muhawarar BBC ta fito da haɗin kan ‘yan siyasar Kano

Yadda muhawarar BBC ta fito da haɗin kan ‘yan siyasar Kano

248
0

Muhawarar da BBC ta gudanar – tsakanin ‘yan takarar gwamna a jihar Kano da ke arewacin Najeriya – ta ƙara fito da yadda ‘yan sisayar jihar ke da haɗin kai da zumunci da mutunta juna a tsakaninsu.

A lokacin gudanar da muhawarar an ga yadda ‘yan takarar suka riƙa mutunta junansu tare da kiran mabiyansu da su gudanar da siyasa ba da gaba ba.

BBC ta shirya muhawar ne tare da gudanar da ita domin bai wa ‘yan takarar damar baje-kolin manyan manufofinsu ga miliyoyin mabiyansu.

Muhawarar ta nuna yadda sannu-a-hankali siyasar jihar ke sauya salo zuwa siyasa ba da gaba ba.

Ɗaya daga cikin ‘yan takarar ya bayyana yadda BBC ta sauke su a ɗaki ɗaya a lokacin da suka halarci taron muhawarar, ya kuma bayyana wa taron muhawar yadda suka gaisa tare da mutunta juna gabanin fara muhawarar.

Wanda kuma hakan ya nuna ƙarara yadda suka ji daɗin hakan, har ma daga ƙarshe yake kira ga mabiyansu da su yi siyasa cikin mutunta juna ga girmamawa.

‘Zan ɗora a kan ayyukan kakana da babana’

Da yake magana a kan batun harkar lafiya a matakin farko, ɗan takarar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna Ya ce ‘Kano ita ce ta ɗaya a inganta harkar lafiya a matakin farko tsakanin jihohin arewacin ƙasar.

Kuma gwamnan jihar mai ci ya ”ɗora ne a kan abin da kakansa Malam Ibrahim Shekarau, ya ɗora akan aikin babansa Injiniya Rabi’u Musa ƙwankwaso, kuma yanzu ga shi yana so ya bai wa ɗansa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna”.

Haƙiƙa waɗannan kamalmai na Gawuna sun nuna tsantsar ɗabi’ar girmama wa da mutunta juna da ‘yan siyasar jihar suka runguma.

Domin kuwa kalaman nasa suna ɗauke da yabo ga tsofaffin gwamnonin jihar waɗanda a yanzu suke cikin jam’iyyu mabambanta.

Saɓanin abin da aka saba gani a harkokin siyasar ƙasar inda waɗanda suke kan mulki ke ƙoƙarin sukar waɗanda suka gada duk kuwa da irin aikin da suka yi.

Tayar juna a lokacin muhawarar

A lokacin muhawarar an ga yadda ‘yan takarar ke tayar da juna a lokacin da suke jawabai, musamman idan suka samu tuntuɓen harshe a lokacin gabatar da muhawar.

Misali a lokacin da ɗan takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf, ke yin bayani game da ƙidddigar asibitoci da likitocin da jihar ke da su, an ga yadda Sha’aban Ibrahim Sharada ɗan takarar jam’iyyar ADP ke taya shi lissafin alƙaluman da yake ƙoƙarin yin bayaninsu.

Wanda kuma hakan ya ƙara fito da yadda ‘yan takatar ke da haɗin kai da fahimtar juna a tsakaninsu

A yi wa juna gaskiya da adalci

A jawabinsa na kammalawa a taron muhawarar ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar PDP Mohammed Sani Abacha ya ce ”ina kira ga al’ummar jihar Kano da su duba Allah su yi wa juna gaskiya da adalci saboda makomar jihar”.

”Da mu da iyayen da ‘ya’yanmu da jikokinmu, da sauran al’ummar Kano da Najeriya ya kamata kowa ya zauna ya yi wa kansa hukunci saboda gaba” a cewarsa.

Ko shakka babu wadannan kalamai ne da ke nuna haɗin kai da mutunta juna.

‘Mu yi siyasa ba da gaba’

Shi ma ɗan takarar jam’iyyar ADP sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya ce ”Kamar yadda yayana ya faɗa, haƙiƙa mun zauna mun kuma mutunta juna, kuma haka muke fata mu yi siyasa ba da gaba ba, ba da daba ba”.

Ya kuma ce jam’iyya ba ta bambanta mutum, dan haka ya ce idan Allah bai ba su nasara ba, zai bai wa duk wanda ya ci zaɓe kundin da ya tanadar domin ciyar da Kano gaba.

Domin a cewarsa ”al’adarmu ɗaya, yarenmu ɗay, addininmu ɗaya kuma garin mu ne, dan haka za mu ɗauko wannan kundi mu miƙa masa, idan yana buƙatar mutanen da muka yi aikin haɗa wannan kundi da shi, za mu ba shi”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here