Home Tsaro Yadda Mu Ka Fahimci Sabon Salon Neman Kudin Fansa Ya Koma Cire...

Yadda Mu Ka Fahimci Sabon Salon Neman Kudin Fansa Ya Koma Cire Sassan Jikin Dan’adam – In Ji Sanata Siyako

98
0
Sen. Siyako, Gombe

Dan Majalisar Dattawa mai Wakiltar Gombe ta Kudu, Sanata Yaro Anthony Siyako ya ce da yawa da ga cikin Yan Majalisar Dattawa ba su san cewa sabon salon da a ke amfani da shi yanzu idan an kama mutane domin neman  kudin fansa shi ne a cire sassan jikin su ba, kamar yadda Hafsoshin tsaro su ka sanar da su a ganawar da su ka yi da su  a ranar Talata.

“ kashewa da cire sassan jikin dan adam wani sabon a bu ne da mafi yawa da ga cikin Yan Majalisar Dattawa su ka fahimci a na amfani da shi a halin yanzu a lokacin da a ka kama mutane domin neman kudin fansa. Wannan sabon a bu ne da ba mu san da shi a baya ba. Kuma ya kamata Yan Najeriya su sa ni sabo da su dau ki matakin da ya da ce”.

Sanata Siyako wanda ya ke yiwa Yanjarida karin haske ga me da zaman da Majalisar Dattawa ta yi da Hafsoshin Tsaro ranar Talata ya ce sha fe awa goma da Majalisar ta yi ta na ganawa da Jami’an ya sa sun fahim abubuwa da yawa wadanda wa sun su ba zai yiwu a sanar da su a kafafen yada labarai ba amma wannan ba tu na cire sassan dan adam ya zama waji bi a sanar da Yan Najeriya domin su san halin da ake ciki.

Sanatan ya ce dalilin da ya sa Majalisar ta gaiyaci Hafsoshin Tsaron da Mai bawa shugaban Kasa Shawara akan harkar Tsaro da Shugaban Jami’an Farin Kaya da Ministan Kudi da sauran su, sa bo da Majalisar ba ta so a yi kom gaba kom baya wajen magance matsalar tsaro da ta addabi kasarnan.

Ya ce, hada wadannan kusoshi guri guda domin tattaunawa da su a kan matsalar tsaro ba karamar nasara ba ce ba da Majalisar ta sa mu wacce ba a taba samun irin ta ba a baya. Kuma ya na da kwarin gwiwa cewa wannan zama zai kawo gagarumar nasara a yaki da a ke yi da ta’addanci a kasarnan.

Siyako ya kara da cewa sun ja hankalin Hafsoshin a kan bukatar da a ke da ita na su yi aiki tare ta hanyar bayar da bayanai na sirri da hadin kai ga junan su domin samun nasarar yaki da ta’addanci kamar yadda Majalisar ta gaiyaci Ministan kudi da sauran ma su ruwa da tsaki akan harkar tsaro domin dode duk wata kafa da zata hana ruwa gudu.

Sanatan ya ce Majalisar ta lura da cewa matsalar tsaro ta na da alaka da abubuwa da yawa kamar yunwa da talauci da rashin aikin yi da tsadar rayuwa da karancin abinci da tsadar sa, da sauran su. Sabo da haka dole kowanne bangare ya bayar da gudunmawar sa idan a na so a sami nasara.

Siyako ya kara da cewa Majalisar Taraiya ta 10 ta himmatu fiye da dukkan Majalisu da aka yi a baya na ganin an sami gyara a kasarnan ta fannin tsaro da tattalin arzikin kasa. Shi ne dalilin da ya sa Majalisar ta gaiyaci ma su ruwa da tsaki akan harkar tattalin arzikin Kasa satin da ya gabata domin su ji da ga ga re su na matakai da su ke dauka na samawa Yan Najeriya sauki na matsin tattalin arzikin Kasa da su ke ciki.

Sanata Siyako ya ce, Majalisar Dattawa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sauke hakkin da ya ke kanta na yin bibiya a kan duk kannin wadan a ka dorawa jagorancin jama’a a fannoni da dama. In da ya ce a matsayin sa na mataimakin Shugaban Kwamitin Yan Najeriya da su ke Kasashen waje, ya je Legas har sau biyar a watan da ya gabata a wani mataki na bibiya a kan aikin da aka dora masa.

Da ga karshe ya yiwa Yan Najeriya albishir cewa wadannan matsaloli da a ke fuskanta na tsaro da matsi na tattalin arziki za su zamo tarihi, sa bo da matakai da Majalisar ta ke dauka su na da inganci so sai. Wanda ya ce gaiyatar dukkanin ma su ruwa da tsaki a kan Harkar Tsaro da Tattalin arziki manuniya ce na irin yunkurin da Majalisar ta ke yi na samawa kasarnan mafita.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here