Home Siyasa Yadda masana suka auna zaɓen gwamnan Kogi da Imo da kuma Bayelsa

Yadda masana suka auna zaɓen gwamnan Kogi da Imo da kuma Bayelsa

191
0
Yantakara Kogi Imo Bayelsa

A Najeriya, masana da masu sa ido a kan zabe na cigaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da yadda hukumar zabe ta gudanar da zaben gwamna a jihohin Imo da Bayelsa da kuma Kogi a karshen makon jiya.

Wasu dai na ganin hukumar ta yi abin a yaba, musamman wajen tabbatar da tsaro ga masu zabe. Sai dai sun ce akwai kurakuren da aka tabka, wadanda ke bukatar gyara, matukar ana so a kayautata zabuka a nan gaba.

Saɓanin yadda aka saba da yi wa hukumar zaɓe caccaka da suka a kan yadda take gudanar da zabe a Najeriya, a wannan karon, da dama daga cikin masu sa ido a kan zaɓe a kasar na ganin cewa hukumar ta yi abin a yaba ta fuskar shiri.

Mallam Awwal Musa Rafsanjani shi ne shugaban gamayyar kungiyoyin farar-hula da ke sa-ido a kan zabe, wanda ya ce na samu sauyi:

Ya ce ‘‘An buɗe runfunan zaɓe a kan lokaci, ta kawo kayayyakin zaɓe a kan lokaci, ta tabbatar da amfani da na’urarar BVAS kuma sun taimaka wajen samar da ingancin zaɓen’’

Wasu masana siyasa ma a Najeriya, irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge na jami`ar Bayero ta Kano na ganin cewa hukumar zabe ta tabuka abin kirki wajen hada kai da jami`an tsaro don samar da kariya ga masu zabe.

”Sun ɗan bada mamaki, kafin zaɓen an samu ɗan tashin hankali a jihohin Kogi da Imo to sai gashi an yi zaɓukan kuma tsoron da ake yi bai faru ba”- Inji farfresa Fagge.

ƘALUBALE:

Sai dai duk da wannan yabon, Mallam Awwal Musa Rafsanjani, ya ce har yanzu akwai matsalolin da ke cigaba da dabaibaye harkar zabe wadanda suka nuna kan su a zabukan da aka yi a jihohi ukun, da ke bukatar gyara:

”Yadda ake ci gaba da cinikin ƙuri’u, ake bada abinci, wani lokacin ma a bada ƴan kuɗn da basu taka kara sun karya ba don a siya ƙuri’a. Wannan yana kawo matsala ga ingancin zaɓe kuma ya saɓa dokokin zaɓe” Inji Rafsanjani

Wata matsalar da masana suka hango ita ce ta rashin fitar masu zabe wajen kada kuri`a. Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce babban koma-baya ne idan aka yi la`akari da dawainiyar da ake yi wajen shirya zabe.

Ya ce ”Shirye-shiyen da ta yi, da irin maƙudan kuɗin da aka kashe kan waɗannan zaɓukan, gaskiya kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba, domin ana zaton ganin tasirin mutane a wajen zaɓen amma basu fito ba, wanda ya nuna cewa mutane sun fara dawowa daga rakiyar zaɓen”

MAFITA:

Masana siyasa da masu sa ido a kan zaben dai sun bayyana cewa akwai bukatar mahukunta su dauki wasu matakai a zahiri don daga martabar zabe a Najeriya, ciki har da tabbatar da bin dokokin zabe da nuna halin ba sani ba sabo wajen hukunta masu aikata laifuka a lokacin zabe….suna cewa bai kamata ana magana kusan shekara ashirin biyar da komawar Najeriya ga turbar demokuradiyya, hukumar zabe na shirya zabe amma ana maimaita kurakuran da aka saba tabkawa ba. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here