Home Siyasa Yadda Majalisar Dattawa Ta 9 Ta Yi Bankwana Da Yan Najeria

Yadda Majalisar Dattawa Ta 9 Ta Yi Bankwana Da Yan Najeria

211
0

Majalisar Dattawa ta 9 ta shafe awa goma jiya Laraba ta na bankwana da Yan Najeriya da kuma junan su in da Yan Majalisar su 109 ko wannen su saida ya tsaya a zauren Majalisar ya na furta irin nasarori da kalubale da su ka fuskanta cikin shekaru 4 da suka yi suna  gudanar da Majalisar.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan wanda ya shafe minti 40 ya na jawabi yace Majalisar ta 9 ta gamu da kalubale masu yawa tare da nasarori masu dunbun yawa.

Da ga cikin nasarorin da Majalisar ta samu sun hada da gabatar da kudure kudure har guda 1,129 a inda da ga cikin su sun sami nasarar amincewa da sama da dari 500. Kuma tsohoh Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sakawa kudure kudure 129 hannu wanda hakan na nufin sun zama doka a Najeriya.

Ahmad Lawan ya kara da cewa da ga cikin wadannan kudure kudure da suka yi nasarar amincewa da su kuma shugaban kasa ya saka masu hannu akwai wadan da za su kawo gagarumin cigaba ga Yan Najeriya a cikin shekara daya zuwa uku masu zuwa.

Kudurorin sun hada da na Mai wanda ake kira da “PIB Bill” da na daidaita kasafin Kudi da na Gyara Kundin Tsarin Mulkin Kasa da na Gyaran sharia da kuma na Yan Sanda da Sauran su.

Har ila yau, Sanata Ahmad Lawan ya ce da ga cikin Yan Majalisa ta Tara an sami wasu da ga cikin su sun sami mukamai a sabuwar gwamnati da aka kafa. Inda ya ce, Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya sami nasarar Zama babban hadimi na Shugaban Kasa wato “Chief of Staff” sai kuma ita ma uwar gidan Shugaban Kasar wacce da ga cikinsu ta ke, wadda it ace mace ta farko a Najeriya wato “First Lady”, Sanata Remi Bola Ahmad Tinubu.

Sai kuma Sanata Gearge Akume wanda ya zama Sakataren Gwamnatin Taraiya da Sanata Uba Sani da ya zama Gwamnan Jihar Kaduna da Karin wasu sanatocin da suka sami mukamai daban daban a Najeriya.

A  bangaren bakin ciki kuma shine rashi na yan Majalisu guda hudu da Majalisar ta yi acikin shekaru hudu da suka yi suna gudanar da ita. Akwai Marigayi Sanata Ignetious Lonja da ga Jihar Plateau da Sanata Rose Oko da ga Jihar Cross River da Sanata Adabayo da ga Jihar Lagos sai kuma Sanata Benjamin dag a Jihar Imo.

Majalisar ta yi shiru na tsawon minti daya domin tunawa da Yan Majalisun guda Hudu da suka rasa rayukansu lokacin Majalisar.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar ta Dattawa Sanata Ibrahim Gobir a hirarsa da Yan Jaridu ya ce Majalisa ta 9 ita ce wacce tafi dukkannin majalisu da aka yi baya a bisa dumbin nasarori du ba da irin kudure kudure da suka sami nasarar amincewa da su kuma shugaban Kasa ya saka masu hannu.

Ya lissafa guda uku da ga cikin su kamar na Mai wato “PIB”, da na Tsarin Mulki wato “Constitution Amendment Bill” da Kuma na Yan Sanda wato “Police Act Amendment Bill”. Inda ya ce wadannan kudure kudure suna da mutukar muhimmanci ga Yan Najeriya.

Sanata Gobir ya ce nan da shekaru biyu zuwa uku za a ga tasirin wadannan kudure kudure ta fannin kawo cigaba ga kasa baki daya.

Shima Sanata Barau Jibrin da ke wakilta Kano ta Kudu ya baiyana nasarori da Majalisar ta Tara ta samu irin kudure kudure da aka amince da su ta fannin Ilimi na kirkiro Jami’o’i da zasu kawo cigaba a fannoni da dama a kasarnan da sauran kudure kudure masu mahimmanci da za su kawo gyara a fannoni  da yawa kamar “PIB Bill” wanda ya ce zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya da Yan Najeriya.

Sanata Barau ya shawarci Yan Majalisu masu zuwa a Majalisa ta Goma da su su yi koyi da irin kokarin da Majalisa ta 9 tayi domin su dora da ga in da ta tsaya domin cigaban Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here