Home Mai da Iskar Gas Yadda maƙwabtan Najeriya suka shiga tasku bayan cire tallafin man fetur

Yadda maƙwabtan Najeriya suka shiga tasku bayan cire tallafin man fetur

228
0

Cire tallafin man fetur da Najeria ta yi ya shafi ɓangarorin rayuwa da dama hatta a ƙasashen da ke makwabtaka da ita.

A ranar 29 ga watan Mayu ne, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur ɗin a lokacin da yake jawabinsa na farko, matakin da ya haifar da tashin farashin man fetur.

A baya dai, farashin man fetur a hukumance bai kai Naira 200 ba a kan duk lita ɗaya ba a Najeriya.

Sai dai labarin cire tallafin ya haifar da hauhawar farashin man zuwa sama da naira 500 a kan kowacce lita.

Abin da kuma ke faruwa kenan a ƙasashe masu maƙwabtaka da Najeriyar, kamar Jamhuriyar Benin da Nijar da Kamaru da sauran su.

Ya lamarin yake a Jamhuriyar Nijar?

A Jamhuriyar Nijar, alƙaluma sun nuna cewa kashi 70 cikin 100 na man fetur din da al`ummar ke amfani da shi na fitowa ne daga Najeriya.

Haliru Yarima, wani mazaunin garin Maraɗi ya ce “gaskiya mu nan mutanen Maraɗi, Jamhuriyan Nijar mun shiga wani irin hali da muka daɗe ba mu shiga irin shi ba a kan abin da ya shafi man fetur.”

‘Domin galibin abubuwan hawanmu, su mashina, motoci da ke amfani da man fetur, mun ta`allaƙa da shi ne na Najeriya.”

“Toh, kai tsaye ana cewa an cire tallafin man fetur sai da mai ya zama dalar CFA 120 a nan Maraɗi, har gara ma ka je ka sha man Nijar tunda man Nijar yana kamawa a kan dalar CFA 108 a gidan mai inda za ka ga layi ya yi yawa.”

Shi kuma Haruna Kanwa, mazaunin birnin Ƙwanni, shi ma ya ce “toh wallahi mun samu illoli bisa ga cire tallafin man da aka yi.”

“Da lokacin nan muna shan mai lita daya a kan dalar CFA 50 amma yanzu ya kai har dalar CFA 110, kuma duk inda ka je, layin mai ne sosai, kaya duk sun yi tsada.”

“Gaskiya cire tallafin nan ya kawo mana illa ƙwarai.”

Wani mai nazari kan al’amuran yau da kullum, Yusufu Abubakar Kaɗo shi ma ya ce “Wannan tallafin man da aka fidda a Najeriya, matsalar mu yan Nijar da za mu samu a kan kayan da za su zo mana daga Najeriya, su za su yi tsada.”

“Tunda tallafin a kan man fetur ne, kamfanonin Najeriya a kan man fetur suke aiki, saboda haka dole kayan da za su sayar mana su yi tsada.”

“An saba kasuwanci da Najeriya tun turawa ba su zo ba muke kasuwanci tsakanin mu kuma yana amfani gare mu.”

“Kasuwanci zai gurɓace tsakanin mu.”

A Benin fa?

A Benin kuma, al’ummar ƙasar su ma sun ce tashin farashin mai ya shafe su ƙwarai da gaske, inda suka ce abin ya ta’azzara kuma sai a hankali.

Alhaji Yusuf daga Kwatano ya ce “Mu gidan mai wasu ɓangeran a Kwatano, yanda ake sayar da mai, haka take, kan CFA 600, matsalar da aka samu a Kwatano shi ne masu zuwa suna sayo mai a Najeriya su zo su siyar a nan, wanda ake cewa `black market` ita ce ta hau a nan Kwatano.”

“Da abin da muke sayen man fetur dalar CFA 70 ne, wani wuri dalar CFA 80, to yanzu dalar CFA 140 muke sayen mai, wasu wuraren ma dalar CFA 160 ne”

“Tun ranar da aka cire wannan tallafin man, kashe-gari muka tsinci kanmu cikin ƙuncin man fetur” in ji wani ɗan kasuwa.

Mamman Ƴamare shi ma ya nuna damuwarsa, inda ya ce “wannan cire tallafin mai ya shafe mu, kawai kwatsam muka tashi wai kudin mai ya haura daga CFA 600 zuwa CFA 700, CFA 800, yanzu ma ya kusan shiga CFA 1000.”

“Kafin cire tallfin man ma, da wahala wasu suke sayen man fetur a kan CFA 400, to yanzu ya kai har CFA 800.”

“Wannan tsadar mai gaskiya ba mu ji dadin sa ba.”

Jamhuriyar Kamaru

A jamhuriyar Kamaru kuwa, kamar yadda wakilin BBC Hausa, Muhammad Babalala ya ruwaito, cire tallafin man fetur ɗin na Najeriya ya yi tasiri a sassan kasar ta Kamaru.

Lamarin ya yi ƙamari a birnin Garoua inda matuƙa babura suke kokawa kan tsadar man fetur a yanzu haka.

Kusan dukkanin harkokin da ake gudanarwa a Garoua na da alaka da Najeriya saboda kusancin da ke tsakanin Kamaru da Najeriya ta wannan bangaren.

Haka nan kusan dukkanin kayan da ake amfani da su a Garoua daga Najeriya ake shiga da su, har da tataccen man fetur wanda ababen hawa ke amfani da su.

Ɗaya daga cikin shugabannin ƴan acaɓa a Garoua, Mamman Sani, ya ce tsadar man fetur a Najeriya ta haifar musu matsala da yawa, inda ya ƙara da cewa “idan abin bai canza ba to harkokinmu za su tsaya cak.”

Sani ya ce yanzu sana’ar babu riba, kuma ya fara tunanin sauya sana’a matuƙar lamarin ya ɗore a haka.

Shi kuma wani mai suna Aliyu ɗan Mallam Sa’adu ya ce “Gaskiya muna shan wahala a wannan aiki, a baya a nan Garoua muna shan litar mai kan naira 300, amma yanzu litar mai ta kai har naira 1,000, abin ya fi ƙarfinmu.”

Ya ƙara da cewa da dama daga cikin su sun fara sayar da baburan da suke haya da su.

Matakin soke tallafin man fetur a Najeriya ya samo asali ne daga makudan kudaden da gwamnati ke kashewa.

Duk da kasancewar Najeriya mai arzikin danyen mai, tana shigo da mafi yawan man da take amfani da shi ne daga waje.

Wannan lamari ne ya sanya sabuwar gwamnati ta gane rashin amfani da tallafin tare da daukar matakai domin sauya yanayin. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here