Home Siyasa Yadda Kyari ya maye gurbin Abdullahi Adamu a matsayin shugaban APC

Yadda Kyari ya maye gurbin Abdullahi Adamu a matsayin shugaban APC

228
0
Adamu Kyari

Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa bayan kwashe shekara daya da ‘yan watanni yana jagorantar jam’iyyar.

Sabon shugaban riƙo na jam’iyyar, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbabar da murabus din Adamu kwana guda bayan kafafen yada labarai a Najeriya sun wallafa rahotanni cewa rashin jituwa tsakanin shugaban na APC da gwamnatin Bola Tinubu ne ya tursasa masa sauka daga kujerar.

Kwamitin gudanarwa na APC din a zamansa na ranar Litinin ya kuma amince da naɗa Sanata Abubakar Kyari wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar a ɓangare arewacin Najeriya a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar.

A watan Maris ɗin 2022 ne aka zaɓi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa bayan gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi shugaban riƙo na kusan shekaru biyu.

‘Takun-saka da Tinubu’

A watan Yunin 2022, ana jajibarin zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da cewa sun yanke shawarar goyon bayan Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda zai riƙe tutar APC a zaɓen 2023 kuma shi ne zai kasance ɗan takarar maslaha.

Lamarin ya tayar da ƙura a tsakanin ƴan siyasa inda waɗansu da dama suka nuna cewa bayan shugabancin Buhari na shekara takwas ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya.

Daga bisani tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaben fitar da gwanin kuma ya zama dan takarar APC a zaben da aka yi a farkon wannan shekarar.

Tinubu ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a karshen watan Mayu.

Tun daga lokacin ne rahotanni ke cewa ana zaman doya da manja tsakanin Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu da kuma fadar shugaban kasa, kuma hakan bai rasa nasaba da abin da ya sa Adamun ya yar da ƙwallon mangwaro ya huta da kuda.

Ko a farkon wannan watan ma, Sanata Abdullahi Adamu ya yi ɓaɓatu game da cikon shugabannin da aka sanar na majalissun dokokin kasar, inda ya nuna rashin gamsuwa da zaɓen da aka yi na masu rinjaye da mai tsawatarwa da wadansu mukaman wadanda ya ce ba a tuntuɓe su ba kafin yanke shawara.

Wane ne Sanata Abubakar Kyari?

Sanata Abubakar Kyari ya shafe kusan wa’adi biyu a matsayin dan majalisar dattawa da ke wakiltar Borno ta arewa, wato daga shekara ta 2015 zuwa 2022 kafin a zaɓe shi a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Ya rike mukamin kwamishina a ma’aikatu da dama a jihar Borno karkashin gwamnatin Sanata Ali Modu Sherrif da kuma Sanata Kashim Shettima.

Kyari ya taba zama dan majalisar wakilai sannan ya rike mukamin shugaban ma’aikata a fadar gwamnatin jihar Borno.

Mai shekaru 60 da haihuwa, Sanata Kyari ɗa ne ga gwamnan mulkin soja na tsohuwar jihar tsakiyar arewa, Birgediya Janar Abba Kyari.

Ya yi karatun firamare da sakandare a jihar Kaduna sannan ya yi digiri na farko da na biyu a kasar Amurka. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here