Home Labaru masu ratsa Zuciya Yadda kwangilar binne gawarwakin ‘masu zanga-zangar Endsars’ ta fusata ‘yan Najeriya

Yadda kwangilar binne gawarwakin ‘masu zanga-zangar Endsars’ ta fusata ‘yan Najeriya

164
0
END SARS

Wata takardar yarjejeniyar binne gawarwaki 103 tsakanin gwamnatin jigar Legas da wani kamfani, da aka bankado a karshen mako na neman tayar da zaune tsaye.

Takardar, ta kunshi wata kwangila ce da ma’aikatar lafiya ta jihar Legas ta bai wa wani kamfani a kan kudi naira miliyan 61,285,000.

Kuma takardar ta bayyana karara cewa an bayar da kwangilar ce domin binne gawarwaki 103 na mutanen da suka mutu a zanga-zangar Endsars da ta faru a shekarar 2020.

Tun farko mutane sun yi tunanin cewa takardar da aka gani tana wadari a shafukan sada zumunta ta bogi ce, to amma bayanin da gwamnatin jihar Legas ta fitar da yammacin ranar Lahadi ya tabbatar da sahihancinta.

Sai dai cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin jihar ta Legas ta ce gawarwakin ba na mutanen da ake zargin sun rasa ransu a mashigin Lekki ba ne, wato Lekki tollgate.

Sanarwar ta kara da cewa “Bayan zanga-zangar Endsars, da rikici tsakanin al’umma a unguwannin Fagba, Ketu, Ikorodu, Onota, Ekporo, Ogba, Isolo da Ajah, hukumar kula da muhalli da lafiyar al’umma ta jihar Legas ta tsinto gawarwakin mutane, ciki har da na yunkurin balle gidan yari na Ikoyi.”

“Gawarwaki 103 da aka ambata a takardar na daga cikin wadanda rikici ya rutsa da su ne a wadannan wurare, ba daga gadar Lekki ba, kamar yadda ake zargi.”

Gwamnatin ta jihar Legas ta ce masu neman tayar da zaune tsaye ne kawai ke kokarin yi wa shirin yin jana’izar mummunar fassara..

Labari ya fara bazuwa ne a cikin karshen mako cewar gwamnatin Legas na shirin yin jana’izar mutanen da aka kashe a lokacin zanga-zangar Endsars, bayan da wani mutum ya wallafa takardar a shafinsa na twitter.

A watan Oktoban 2020 zanga-zanga ta balle a Legas da ma wasu biranen Najeriya domin nuna adawa da ‘zaluncin’ jami’an ‘yan sandan SARS, lamarin da daga baya ya kazance ya so ya koma tarzoma.

Lamarin ya yamutse ne bayan bata-gari sun kwace zanga-zangar ta Endsars, suka fara fashe-fashe da barnata dukiyar gwamnati da ta al’umma.

Labari ya sha banban bayan da aka zargi jami’an tsaron Najeriya da bude wuta a kan masu zanga-zanga da misalin karfe 6:45 na yammacin wata ranar Talata a kan gadar Lekki da ke birnin na Legas.

Kungiyar Amnesty international ta yi zargin cewa sojojin Najeriya sun kashe akalla masu zanga-zangar lumana 12.

Gwamnatin jihar ta Legas dai ta sha musanta zargin, haka nan ma rundunar sojin ta Najeriya. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here