Home Siyasa Yadda kotun zaɓen shugaban ƙasa ta kori ƙarar Peter Obi

Yadda kotun zaɓen shugaban ƙasa ta kori ƙarar Peter Obi

193
0
Kotun Daukaka Kara

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta kori ƙarar Peter Obi da jam’iyyarsa LP, da ke ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu na jam’iyyar APC.

Mai shari’a Haruna Tsammani ne ya gabatar da hukuncin, yayin dogon zaman kotun a ranar Laraba.

Kotun dai ta yi watsi da manyan ƙorafe-ƙorafe guda uku da Peter Obi da kuma jam’iyyarsa ta LP suka shigar.

Yayin gabatar da hukuncin alƙalan kotun biyar, kotun ta yi watsi da bahasin wasu shaidu guda 10 cikin 13 da ɗan takara Peter Obi da jam’iyyar LP suka gabatar.

Haka kuma, Mai shari’a Tsammani ya ce kotun ta ƙi amincewa da iƙirarin masu ƙorafi na cewa an yi aringizon ƙuri’u a jihohi irinsu Yobe da Oyo da Kano da sauransu, saboda ba su gabatar da bayani a kan tasoshin zaɓen da al’amarin ya faru ba.

“Hankali ba zai ɗauka ba cewa, mai ƙorafi ya yi zargin maguɗi a wurare masu yawa cikin tasoshin zaɓe 176,000 da mazaɓu sama da 8000 na ƙananan hukumomi 774 a cikin jiha 36 da kuma Abuja, amma ba tare da ya zayyana taƙamaimai wuraren da aka yi maguɗin da ya yi zargi ba,” kotun ta ce.

Hukuncin ya kuma ce jam’iyyar LP ta gaza kafa hujja kan iƙirarin da ta yi, na samun kura-kurai a zaɓen watan Fabrairu.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa hukumar zaɓe ta INEC ta rage mata ƙuri’un da ta ci, inda ta ƙara a kan ƙuri’un jam’iyyar APC, sai dai a cewar kotun, jam’iyyar LP ta gaza gabatar da cikakken bayani a kan haƙiƙanin yawan ƙuri’un da ta ci, kafin a rage mata su, kamar yadda ta yi iƙirari, kuma ba su iya ba da bayani a kan tashoshin zaɓen da hakan ta faru ba.

Sai dai, kotun ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta da hurumin ƙalubalantar matsayin Peter Obi na kasancewarsa, ɗan jam’iyyar LP.

Tun faro, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta yi watsi da ƙarar da ke neman a soke cancantar Kashim Shettima, a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Mai shari’a Haruna Tsammani ne ya tabbatar da haka lokacin da yake karanto hukunci a kan ƙorafe-ƙorafen jam’iyyar APM, da ke ƙalubalantar zaɓen Bola Ahmed Tinubu na APC.

Kotun dai ta ce kori matakin ƙalubalantar cewa an ba da sunan Kashim Shettima, don zama ɗan takara har sau biyu ba.

Jam’iyyar APM ta ƙalubalanci matakin ba da sunan Shettima ne a matsayin ɗan takarar sanata a jihar Borno, kafin a sake bayar da sunansa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.

Tun farko, kotun ta kori ƙorafin APM da ke neman soke cancantar tsayawa takara ga Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Yana ɗaya daga cikin hukunce-hukunce guda uku da kotun take yankewa a Larabar nan.

Ana kallon hukuncin a matsayin jagora a jerin hukunce-hukuncen zaɓukan gwamnoni na watan Maris, waɗanda alƙalai daban-daban suka saurara a matakan jihohi, kuma nan gaba ne su ma za a sanar da sakamakon ƙararrakin.

Ba shakka, lokaci ne mai cike da zulumi da zaman ɗar-ɗar aƙalla ga ‘yan siyasa da magoya bayansu.

Hukumomi sun ce sun ɗauki matakai don tabbatar da doka da oda a lokacin sanar da hukuncin da kuma bayan hakan. ‘Yan sanda sun ce sun ƙara tura jami’ansu sassan Najeriya don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Cikin amo mai ƙarfi, rundunar ‘yan sanda ta ja hankalin waɗanda ta kira ‘yan jamhuru da jiga-jigan siyasa, a kan su yi hattara wajen furta kalamai da ayyukansu, don kuwa ba za ta lamunci iza wutar tarzoma ko abin da zai jefa ƙasar cikin zaman kara zube ba.

Masharhanta na cewa ba a taɓa soke zaɓen shugaban ƙasa a tarihin Najeriya ba, tun bayan komawar ƙasar tafarkin dimokraɗiyya a 1999.

Sai dai, ga alama hakan ba shi da wani tasiri a dimokraɗiyya da ke ƙara ƙarfi da haɓaka kamar ta Najeriya. A 2015, Muhammadu Buhari ya kafa tarihi irinsa na farko a ƙasar, inda ya kayar da shugaban ƙasa mai ci, Goodluck Jonathan.

Akwai damar ɗaukaka ƙara

Masana shari’a a ƙasar kamar fitaccen lauyan Najeriyar nan, Femi Falana mai lambar SAN na cewa yankan baya da razanarwar da ake yi wa ɓangaren shari’a irin wanda ba a taɓa gani ba game da hukuncin kotu, abu ne da ba shi da wata ma’ana.

Ya ce duk ɓangaren da bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba, to yana da damar ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙolin Najeriya.

Yayin hira da gidan talbijin na Channels TV, Femi Falana ya ce ya damu a kan yadda mutane suke nuna cewa komai ya ƙare a sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa.

A cewarsa, hakan ba gaskiya ba ne.

Duk ɓangaren da bai yi nasara ba, kuma ya ji bai gamsu da hukuncin ba, to yana da damar garzaya wa gaban Kotun Ƙoli. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here