Home Siyasa Yadda Kanawa Ke Zaman Jiran Hukuncin Kotu Kan Zaɓen Gwamnan Jihar

Yadda Kanawa Ke Zaman Jiran Hukuncin Kotu Kan Zaɓen Gwamnan Jihar

171
0
Abba Gidagida Gawuna

Al’ummar jihar Kano, musamman magoya bayan manyan jam’iyyun siyasa biyu na jihar APC da NNPP, sun wayi gari cike da zaƙuwa gabanin sanar da wani hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, nan da ‘yan sa’o’i cikin Juma’ar nan.

Hukuncin kotun, wadda ke zamanta a Abuja, yana da matuƙar muhimmanci ga siyasar jihar, mafi yawan jama’a da harkokin kasuwanci a arewacin Najeriya, kuma ginshiki ne ga makomar siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna, aƙalla tsawon shekara huɗu nan gaba.

Abba Kabir Yusuf ya garzaya gaban kotun ɗaukaka ƙara ne, bayan kotun ƙorafin zaɓe ta jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba, ta rushe nasarar da ya samu, inda ta ce abokin takararsa na jam’iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna ne halastaccen wanda ya ci zaɓe.

Kotun ta soke sama da 165,000 a cikin ƙuri’un Abba Kabir Yusuf na NNPP, bisa hujjar cewa ba su inganta ba, saboda rashin sa hannu da kwanan wata da kuma hatimin hukumar zaɓe.

Jam’iyyar APC ta roƙi kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Gwamna Abba Kabir.

Takara tsakanin ɓangarorin biyu, na ɗaya daga cikin mafi zafi da aka gani kafin zaɓen 18 ga watan Maris a Najeriya, kuma ga alama har yanzu, yanayin siyasar bai daina tafarfasa ba, wata takwas bayan kammala zaɓe.

Hukumomin tsaro a Kano, tun farkon wannan mako sun ce sun tura ƙarin jami’ai da kayan aiki zuwa manyan fuskokin garin, don hana faruwar tashin hankali, da kuma kare rayuka da dukiyar al’umma, tun kafin sanar da hukuncin.

Dukkan ‘yan takarar a zaɓen da ya wuce, suna da alaƙa da jiga-jigan ‘yan siyasar Kano biyu, Rabi’u Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje, tsoffin gwamnonin jihar da ke kan ganiyarsu har yanzu, sannan tsoffin manyan aminan juna, kafin su ɓaɓe a tafiyar siyasa.

Rundunar ‘yan sandan Kano dai ƙarƙashin kwamishinanta, Mohammed Usaini Gumel, ta gudanar da taron gaggawa da shugabannin jam’iyyun APC da NNPP a jajiberen wannan rana ta yanke hukunci.

Ta ce sun ɗauki matakai da haɗin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro a jihar don ganin ba a fuskanci rashin zaman lafiya a yayin, da kuma har bayan hukuncin kotun ba.

Kwamishina Mohammed Usaini ya kuma ce, sun tattauna, kuma sun samu tabbaci daga shugabannin jam’iyyun biyu cewa za su yi duk abin da ya wajaba don ganin ba a kawo hargitsi, saboda hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ba a Kano.

APC mai mulkin Najeriya, kuma tsohuwar mai mulkin Kano, tana fatan kotu za ta ba ta gaskiya, kuma ta tabbatar mata da kujerar gwamnan, wadda ta kuɓuce mata, zuwa hannun jam’iyyar adawa ta NNPP, yayin da NNPP ke alla-alla ta tsira da kujerar gwamna ɗaya tilo da ta samu a zaɓen 2023.

Ko ma dai yaya za ta kasance, a ƙarshen zaman kotun na Juma’a, akwai damar sake ɗaukaka ƙara ta ƙarshe ga duk ɓangaren da bai gamsu ba, zuwa gaban Kotun Ƙolin Najeriya, wadda daga kan ta ne, sai dai Allah ya isa.

Hukuncin na zuwa ne kwana goma cif bayan alƙalan kotun da ke zama a Abuja, sun saurari bahasin duk ɓangarorin da ke cikin shari’ar, tare da sanya hukuncinsu a mala.

Mutane har a shafukan sada zumunta na tafka muhawara game da hukuncin da kotun za ta yanke. Ga kadan da muka tsakuro a cikinsu:

Wani mai suna Abdussamad a shafin X wanda aka fi sani da Twitter a baya, ya ce: “Eh, wannan haka yake. Kotun Daukaka Kara za ta sanar da hukuncinta a kan zaben Kano ranar Juma’a da misalin karfe 10 na safe a Abuja. Wannan hukunci ne da ake matukar tsammanin sauraronsa, don kuwa sakamakon na da gagarumin tasiri ga siyasar jihar Kano.”

Sai Suleiman Mas’ud wanda ya ce” “Ko yaya hukuncin kotun zai kasance, ina fatan ba za a samu tashin hankali a Kano ba, duba da yadda adawa ta yi zafi tsakanin magoya bayan dukkan jam’iyyun.”

Me ya faru a kotun korafin zaɓe?

Kotun Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, shugabar da ta jagoranci alƙalan kotun guda uku ta soke nasarar Abba Kabir ne bisa hujjar cewa an yi aringizon ƙuri’u har 165,633, waɗanda aka gano ba su da sitamfi da kwanan wata da kuma sa hannu a cikin ƙurin gwamnan.

Tun farko a watan Maris, hukumar zaɓe ta ce ɗan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓen gwamnan Kano, da ratar ƙuri’a 128,900.

Abba Kabir Yusuf, in ji INEC ya samu ƙuri’u mafi rinjaye har 1,019,602, inda Nasiru Yusuf Gawuna da ke biye da shi, ya samu ƙuri’a 890,705.

Alƙalan ƙaramar kotu, sun umarci hukumar zaɓe ta INEC ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba Kabir Yusuf, tare da gabatar da ita ga Nasiru Yusuf Gawuna. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here