Home Addini ‘Yadda Isra’ila Ta Kai Hare-hare Kan Gidajen Falasɗinawa

‘Yadda Isra’ila Ta Kai Hare-hare Kan Gidajen Falasɗinawa

217
0
ISr 1

Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da mazauna yankuna bakwai na Zirin Gaza cewa su bar gidajensu tare da tafiya tsakiyar birane domin neman mafaka yayin da take ƙaddamar da sabbin hare-hare kan sansanonin mayakan Hamas.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC yadda iyalai ke tururuwa suna barin gidajensu inda suke neman mafaka a makarantu mallakin Majalisar Dinkin Duniya.

Isra’ila ta kai hari kan cibiyoyin Hamas

ISR 2

Dakarun sama na Isara’ila sun saki wani bidiyo da ke nuna yadda makamansu suka sauka kan gine-gine da ke Zirin Gaza, inda aka ce sansanoni ne na sojojin Hamas.

Ta kuma ce jiragen yaƙinta na ci gaba da kai hare-hare kan “muhimman wuraren tafiyar da ayyuka” na Hamas.

An kuma samu rahotannin fashe-fashe a kusa da dogon ginin Watan Tower, wani wuri mai cike da hada-hadar kasuwanci a Gaza.

ISR 3

Aƙalla mutum 250 ne aka ruwaito sun mutu, wasu 1,100 sun samu raunuka bayan ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta ƙaddamar da hari mafi muni a shekarun baya-bayan nan kan Isra’ila.

Gwamman mayaƙa daga cikin Gaza sun kutsa yankunan Yahudawa a kudancin Isra’ila yayin da suke samun kariyar makaman da ƙungiyar ke cillawa ta sama.

Mayaƙan na Hamas yanzu haka suna garkuwa da sojoji da fararen hula ƴan kasar Isra’ila.

Isra’ila ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da miyagun hare-hare ta sama a kan yankin Gaza, inda ta kashe Falasɗinawa 232 tare da raunata wasu 1,600, kamar yadda ma’aikatan lafiya suka bayyana.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra’ila “na cikin yanayi na yaƙi” sannan ya sha alwashin cewa ƙungiyar Hamas, wadda ita ce ke mulkin yankin Gaza za “ta ɗanɗana kuɗarta.”

Rundunar sojin Isra’ila ta taso da dakarunta na ko-ta-kwana, kuma ana sa ran cewa za ta ƙaddamar da samame ta ƙasa.

‘Yaƙi mai tsawo da wahala’

Firaminsitan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya shaida wa al’ummar ƙasarsa cewa “za a shiga wani yaƙi mai wahala da za a daɗe ana yi.”

A wata tattaunawa da jagororin tsaro na gwamnatinsa, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce: “Burinmu na farko shi ne mu kawar da dakarun maƙiya da suka kutso cikin ƙasarmu sannan mu dawo da tsaro da lumana a yankunan da aka kai wa farmaki.”

“Burinmu na biyu a lokaci guda shi ne mu gallaza wa maƙiya a Zirin Gaza.”

“Buri na uku shi ne mu ƙara toshe sauran ƙofofi ta yadda babu wani daban da zai yi kuskuren tsoma kansa cikin wannan yaƙi.”

Wannan ne tashin hankali mafi muni cikin shekaru da aka samu, a wani ɓangare na rashin jituwar da ke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

ISR 4

Wannan karo an ga yadda mayakan Faladinawa suka tsallaka shinge zuwa cikin Isra’ila da sanyin asubahi.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da suke cilla rokoki daga Gaza – inda wasu daga cikin rokokin suka kai har birane masu nisa irin su Tel Aviv da kuma Ƙudus.

Babu cikakken bayani kan yadda mayakan na Hamas suka iya kutsawa ta ɗaya daga cikin kan iyaka mafiya tsaro a doron kasa.

Isra’ila ta ce jiragenta na yaki sun kaddamar da hare-hare ta sama a sansanonin Hamas da ke Gaza, kuma sun samu nasarar samun sansanonin sojin Hamas 17.

Bama-baman da dakarun Isra’ila suka jefa sun lalata wani bene mai hawa 11 a tsakiyar birnin Gaza, wanda ke kunshe da gidajen rediyon kungiyar Hamas.

Kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta Medecins Sans Frontieres ta ce an kashe wata malamar jinya da kuma wani mai tuka motar asibiti sanadiyyar hare-haren na Isra’ila a kan wasu asibitoci biyu na yankin Gaza.

Wasu daga cikin rokokin da Hamas ta harba zuwa Isra‘ila sun samu faɗawa kan gidajen mutane da motoci ne bayan sun shallake shingen kariya daga hare-haren sama na Isra’ila.

Mazauna wasu daga cikin biranen Isra’ila da lamarin ya shafa sun ce sun daɗe ba su tsinci kansu cikin irin wannan hali ba.

An rufe zirga-zirga a hanyoyi da dama na birnin Tel Aviv yayin da garin ya zama fayau.

Amurka na bayan Isra’ila ɗari bisa ɗari – Biden

Biden

Shugaban Amurka a wani jawabi da ya gabatar a fadar White House ya ce “Isra’ila na da ƴancin kare kanta da al’ummarta.”

Ya kuma jaddada goyon bayan Amurka ga Isra’ila, inda ya ce “babu sauyi ko kaɗan game da tsantsar goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra’ila.”

Iran ta nuna goyon bayanta ga Falasɗinawa

Ayotallah

Wani bayani da ya fito daga kamfanin dillancin labaru na Iran ISNA, ya ambato wani mai bai wa jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei na nuna goyon baya ga Falasɗinawa game da harin da suka ƙaddamar kan Isra’ila.

An ambato Rahim Safayi na cewa “Muna taya mayaƙan Falasɗinu murna.”

Ya ƙara da cewa “Za mu ci gaba da mara wa mayaƙan Falasɗinawa baya har sai an ƴantar da Falasɗinu da kuma birnin Ƙudus.”

Isra’ila ta ce mayaƙan Hamas sun yi garkuwa da Yahudawa

BBC ta fahimci cewa mayaƙan Hamas sun yi garkuwa da gomman sojoji da fararen hulan Isra’ila a sabon artabu na baya-bayan nan da ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu.

Wasu na tunanin cewa, an yi musu ƙawanya ne a wasu ƙananan garuruwa da ke kusa da Zirin Gaza.

Sai dai jami’an Isra’ila sun musanta rahotannin cewa har da wani babban hafsan sojin rundunar tsaron ƙasar mai muƙamin manjo janar a cikin mutanen da aka sace.

Hamas ta yi iƙirarin cewa ta kama fursunonin yaƙi 53. Rundunar sojin Isra’ila ba ta fayyace a martanin da ta yi ba kan hakikanin ƙarin bayani. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here