Home Kotu da 'Yan sanda Yadda Hukumar Makarantar Jiragen Sama Ta Zariya Ta Sayar Da Sabbin...

Yadda Hukumar Makarantar Jiragen Sama Ta Zariya Ta Sayar Da Sabbin Jiragen Da Aka Saya Dala Miliyan 7, A Kan Miliyan Daya

144
0
IMG 20240121 WA0062

Majalisar Wakilai ta  ce ba zata sabu ba,bindiga a ruwa; za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin wasu sabben Jiragen sama guda biyu da a ka saya don amfanin kasarnan amma Hukumar Makarantar Koyar Aikin Jiragen Sama ta Zariya ta Sayar da jiragen da a ka saya sama da Dalar Amurka Miliyan 7, a kan sama da Dala Miliyan 1.

 

Majalisar ta sha wannan alwashi ne bayan da Kwamitin ta mai Kula da Kadarorin Gwamnati ya fara saurarar badakalar a jiya Alhamis a dakin taro na Majalisar Wakilai.

 

A hirar sa da Yanjaridu jimkadan da kammala zaman ranar, Mataimakin Shugaban Kwamitin Hon. Isma’il Dabo, wanda ke Wakiltar Jama’ar Toro da ga Jihar Bauchi ya ce Majalisar ba za ta yarda b, kayan da a ka saya don amfanin Kasarnan wasu mutane su sayar da shi ba tare da wani dalili ba.

 

Ya ce jiragen sabbi ne kuma ba’ayi wani aiki da su ba, a ka sayar da su duk da cewa Hukumomin Yansanda da Sojojin Kasa da na Sama duk sun ce su na bukatar wadannan jirage amma a ka ki ba su wadannan Jirage a ka sayarwa da wasu mutane a Kasarnan.

Hon. Toro

Hon. Toro ya ce bayan da Majalisar ta yi bincike na kanta ta gano cewa lallai an sayar da jiragen ba tare da an bi ka’idoji ba, sabo da haka ne ya sa su ka gaiyaci Shugabannin Hukumar Makarantar don su bincika su gano ainahin abun da ya faru don tabbatar da cewa an hukunta wadanda su ka yi wannan badakala.

 

“ Najeriyan Army sun rubuta sun ce su  na son wadannan Jirage, Navy sun ce su na son wadannan jirage, Police su ma sun ce su na son wadannan jirage amma wannan ma’aikata ta yi kunnen kashi, su ka dau ki wadanan jirage su ka sayar da su ga wasu mutane daban; su ka karya farashin su, su ka sayar da su kamar yadda a ke sayar da gyada”. In Hon. Toro.

 

Sabo da haka ne ya ce Majalisar ta gaiyace su domin su yiwa Majalisar bayani yadda abun ya faru. Domin a matsayin su na wakilan al’umma idan su ka bar irin wannan badakala da wuce haka Allah zai tambaye su kuma Yan Najeriya ma su na da hakki akan wadannan kayayyaki.

 

Ya ce Majalisar ta umarci Shugabannin Hukumar Makarantar da su zo da jerin bayanai na wadanda a ka sayarwa da Jiragen da shedu na takardu da dokar Sayar da kayayyakin Gwamnati ta tanada don tantancewa su, a ga cewa ko an bi ka’ida ko kuma ba a bi ka’idojin ba domin su gabatar da rahoton binciken su ga Majalisar Wakilai don daukar hukuncin da ya da ce.

 

Hon. Toro ya jaddada kwarin gwiwar sa na ganin cewa, Majalisar Wakilai da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu za su yi tsayin daka wajen ganin an hukunta su idan an same su da laifi. Ya ce Shugaba Tinubu ba zai taba goyon bayan wanda a ka samu da cin amanar Gwamnati ba, in da ya bayar da misali da binciken da a ke yiwa Tshohon Shugaban Babban Bankin Najeriya, Godswill Emefeliye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here