Home Siyasa Yadda Hope Uzodimma ya lashe zaɓen gwamnan Imo

Yadda Hope Uzodimma ya lashe zaɓen gwamnan Imo

200
0
IMO GOV. Election

Gwamnan Imo kuma ɗan takarar jam’iyyar APC, Hope Uzodimma, ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.

Gwamnan wanda ya samu wa’adi na biyu a kan karagar mulki ya cinye dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar.

Babban Baturen Zaɓe Farfesa Abayomi Fashina na Jami’ar Tarayya ta Oye Ekiti ne ya bayyana Mista Uzodimma a matsayin wanda ya yi nasara, inda ya ce ɗan takarar na APC ya samu ƙuri’a 540,308.

Ɗan takarar jam’iyyar PDP, Samuel Anyanwu, ya samu ƙuri’u 71,503. Sai kuma Achonu Nneji na jam’iyyar Labour Party da ya samu 64,081.

Tun da misalin ƙarfe 2:00 na dare ranar Asabar aka fara tattara sakamakon zaɓen, wanda ake ganin ya tafi lafiya ƙalau a mafi yawan rumfunan zaɓe duk da faragabar t ashin hankali da aka dinga yi sakamakkon ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here