Home Uncategorized Yadda Bikin Ranar Hausa Ta Duniya Ya Kasance A Jamus

Yadda Bikin Ranar Hausa Ta Duniya Ya Kasance A Jamus

152
0
Hausa German

Yau 26 ga watan Augusta ake bikin Ranar Hausa ta Duniya, Hausawa mazauna Turai sun ci gaba da raya al’adunsu.

Hausawa mazauna Turai ba su gaza ba wajen raya al’adunsu duk kuwa da nisan da suke da shi da kasar Hausa da ma kalubalen da suke cin karo da su daga lokaci zuwa lokaci, a kokarinsu na son ganin sun raya al’adar a kasashen Turai.

To sai dai kuma ba Hausawa kadai ne ke maraba da zuwan wannan rana ba. A yayin da Hausawa ke gudanar da bikin a Turai, wasu daga cikin Turawan Jamus da ke sha’awar koyon harshen na Hausa su ma sun yi tsokaci albarkacin Ranar Hausa ta Duniya.

Wannan dai ya nuna yadda harshen na Hausa ke ci gaba da samun karbuwa a sauran sassan duniya. Sai dai duk da irin wannan ci gaban da aka samu, akwai kalubalen da harshen ke fuskanta sosai musanman a tsakanin Hausawa in ji Malam Ibrahim Muhsin, wani Malami dan Najeriya da ke sashen koyar da Al’adun Afirka a Jami’ar birnin Cologne da ke Arewacin kasar Jamus, ya ke kuma koyawa Jamusawa harshen Hausa.

A daya bangaren kuwa, daya daga cikin kalubalen da wasu daga cikin Hausawa mazauna Turai ke fuskanta shi ne, yadda yaran da suke haifa a Turai suke fuskantar koma baya wajen magana da harshen.

Malam Ado Salifu, wani ‘dan Jamhuriyar Nijar ya shawarci wadanda ke fuskantar wannan matsalar da su tashi tsaye don nema wa matsalar mafita.

Alkaluma dabam-dabam dai sun nuna irin bunkasa da harshen Hausa ke ci gaba da yi a fadin duniya. Bincike na baya-bayan na nuna cewa harshe ne na 11 a wajen girma da yaduwa cikin hanzari a duniya. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here