Home Tsaro ‘Yadda Bam ya kashe Fulani 27 a jihar Nasarawa’

‘Yadda Bam ya kashe Fulani 27 a jihar Nasarawa’

200
0

Jami’an  tsaro a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar aƙalla Fulani 27, yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon tashin bam a wani kauye da ke kan iyakar jihohin Nasarawa da Benue.

A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa Maiyaki Muhammed Baba, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce sun samu labarin faruwar al’amarin ne da safiyar ranar Laraba.

Ya ce “mun tashi da safen nan aka ce mana an jefa bam, ko kuma wani bam ya tashi, akwai gawarwaki da yawa da shanu waɗanda aka yi asara.”

Ya ƙara da cewa yanzu da haka hukumar ƴan sanda na ci gaba da bincike kan lamarin.

Sai dai ya ce ba zai iya cewa komai ba kan ko an jeho bam din ne daga sama ko kuma dasa shi aka yi a ƙasa.

Baba ya ce “Yanzu dai an samu gawa wurin 27, sannan akwai wasu da dama da suka samu raunuka.”

Lamarin ya faru ne a wani ƙauye da ke yankin Doma na jihar Nassarawa.

Ardo Lawal shi ne shugaban fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore a jihar Nassarawa ya ce lamarin ya faru ne bayan fulanin sun karɓi shanu daga hannun hukumomin jihar Benue, tare da baro jihar domin zuwa wani wurin na daban.

Ya buƙaci hukumomi da su yi bincike domin tabbatar da adalci kan lamarin.

Ya tabbatar wa BBC cewa akwai gawa 27 da ke a hannunsu sanadiyyar lamarin, yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti suna jinya.

Jihohin Nassarawa da Benue na daga cikin jihohin yankin arewa ta tsakiyar Najeriya wadanda ke fama da matsalar rikicin ƙabilanci tsakanin manoma da makiyaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here