Home Addini Yadda Al’ummar Musulmi Ke Cigaba Da Shagulgulan Babbar Sallah

Yadda Al’ummar Musulmi Ke Cigaba Da Shagulgulan Babbar Sallah

202
0
Sallah Image

Ranar Larabar aka gabatar da Sallar Layya, a sassan duniya daban-daban, bayan miliyoyin Musulmin da suka je aikin Hajji sun yi hawan Arafa a ranar Talata.

Wani muhimmin abu yayin wadannan bukukuwa shi ne yin layya.

Bayan kammala sallar idi Musulmai masu hali za su yanka dabbobin da suka tanada don yin layya.

Biki ne da ake gudanarwa sau daya a shekara, inda jama’a ke dafa abinci, a ci a sha a yi hani’an, a kuma ziyarci ‘yan uwa da abokan arziki.

Hatta wadanda ba su samu yin layya ba kan yi watanda, wato a hada kudi a sayi wata dabba don a yanka a raba.

Sallah Image 2

Wasu kuwa da Ubangiji bai huwace masu ba sukan samu kyautar nama daga ‘yan uwa da abokan arziki don suma su gurje bakinsu, tun da kamar yadda Hausawa kan ce ne, Sallah biki daya rana.

Baya ga rabon naman da aka yanka na layya, akan kuma yi girki na gani na fada, a kuma yi ta aika wa ‘yan uwa da abokan arziki albarkacin wannan rana.

Ga yara kanana kuwa, a iya cewa wannan lokaci abu nasu ne maganin a kwabe su, duba da yadda a kan gwangwaje su da kwalliyar sabbin kaya na gani na fada.

Su kuma fita yawon salla gidajen ‘yan uwa da abokan arziki a ranakun farko- farko, daga bisani kuma a kai su gidajen wasa da sauran wuraren yawon bude ido don faranta masu.

Me ya kamata Musulmai su yi a wannan rana ?

Akwai muhimman ayyuka na ibada da aka tanada ga kowanne Musulmi a rana irin wannan domin samun dacewar Ubangiji.

Sheikh Yusuf Musa Asadussunnah, malamin addinin Musulunci ne a jihar Kadunan Najeriyar, kuma ya shaida wa BBC cewa babban abin da ake so ga Musulmi a wannan rana musamman ga wanda zai yi layya shi ne da zarar ya wayi gari ya jinkirta cin wani abu har sai an dawo daga masallacin idi.

A cewar malamain ”Sabanin karamar sallah, ita sallar idi ana son a jinkirta cin wani abu, sannan idan za a je masallaci a rika kabarbari, a can masallacin za a saurari huduba, ko da yake ba dole ba ne, mustahabbi ne”.

Ya kara da cewa bayan an kammala huduba an yi sallah ne liman zai yi yankansa, daga nan kuma sai kowa ya je ya yi nasa.

Ya ce ana bukatar kowanne Musulmi ba babba ba yaro ba mace ba namiji, ya halarci sallar idi, domin Annabi (SAW) ya lazumce ta, sakamakon irin alheran da ke cikinta

Dabbobin da za a iya yin layya da su

Sheikh Musa Yusuf Asadussunah ya ce akwai nau’ikan dabbobi kimanin takwas, da za a iya yin layya da su.

Sallah Image 3

Ya ce kamar yadda Allah (SWT) Ya ce ”Akwai sa, da kuma saniya, akwai rago da tunkiya, akwai bunsuru, da akuya, sai kuma rakumi da rakuma”.

Ya ce duk dabbar da aka yi da ita cikin wadannan layya ta yi, sai dai akwai sabani tsakanin malamai sun yi sabani musamman kan girman rago da rakumi, amma dai sun ce Annabi ya fi yi da rago, amma kan batun da ba na layya ba, Annabi ya ma fi ta’ammali da naman akuya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here