Home Tsaro Yadda aka sace masu ibada a Katsina da ƙona babban limamin Cocin...

Yadda aka sace masu ibada a Katsina da ƙona babban limamin Cocin Katolika a Neja

166
0

Ƙungiyar Kiristoci ta CAN a arewacin Nijeriya ta auka cikin jimami da zullumi, tun bayan sace masu ibada a yankin Ƙanƙara na jihar Katsina, da kuma kashe wani babban limanin Kirista a jihar Neja.

Hukumomi a jihar Neja sun ce wasu mahara da ake zargin sun shiga Neja ne daga maƙwabciyar jihar, suka ƙona gidan babban limamin, Isaac Achi na Cocin Katolika tare da shi a ciki, a garin Kafin Koro.

Hukumomin Neja dai sun ce maharan waɗanda ake zargin ƴan fashin daji ne sun faɗa garin da ke ƙaramar hukumar Paikoro, inda suka shiga cocin Saint Peter and Paul Catholic Chuch da wata makaranta da ke kusa.

Sakataren Gwamnatin jihar ta Neja, Ahmed Matane, ya ce babu tabbacin ko ƴan fashin dajin sun yi awon gaba da mutane bayan da suka yi aika-aikar.

“Abin baƙin ciki su ƴan ta’adda sun shigo daga Kaduna, suka raba kansu, suka shiga wannan ƙauyen, suna shiga suka sa wa gidan fasto da makarantun da ke wurin wuta, sannan suka ci gaba da harbi,” in ji Matane.

“Ba mu sani ko sun sake shiga wasu gidaje ba, ko sun ɗauki wasu mutane, wannan babu cikakken bayani.”

Ya kuma yi iƙirarin cewa ƙoƙarin jami’an tsaro na fatattakar waɗannan mahara ya sa ƴan fashin daji ba su da sansani a yankin, amma suna shiga ta dajin Kafin Koro daga maƙwabtan jihohi, inda suke addabar yankunan Rafi da Shiroro da Munya da Paikoro.

A bara ne Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanar da ƙaddamar da gagarumin aikin sojoji a jihar ta Neja, sakamakon ƙazancewar hare-haren ƴan fashin daji da ƴan tada ƙayar baya na Boko Haram.

A wata mai kama da haka, shugaban cocin Katolika na ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina, Ravaran Yusufa Haruna ya tabbatar da sace masu ibada tara a ƙauyen Gidan Haruna.

A cewarsa, maharan sun jikkata mutum ɗaya a harin da suka kai a ƙarshen mako.

Ya ce “ƴan ta’adda sun zo suka same su suka tafi da mutum bakwai da yara guda biyu kuma sun bugi wani da sanda sun karya shi a hannu.”

Neja da Katsina na cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da yawan hare-haren ƴan fashin daji a ƙasar.

Kuma duk da iƙirarin hukumomi cewa suna murƙushe ƴan fashin da sauran ƴan bindiga, har yanzu mazauna ƙauyuka da wasu garuruwan ƙasar na ci gaba da ɗanɗana kuɗa a hannun irin waɗannan ɓatagari. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here