Home Tsaro Yadda Ƴan Bindiga Su Ka Kai Harin Ramuwa A Zamfara

Yadda Ƴan Bindiga Su Ka Kai Harin Ramuwa A Zamfara

160
0
Zamfara Gov. praying

A Najeriya rahotanni daga garin Nasarawar Zurmin a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar sun ce wani ɗan sanda ya rasa ransa yayin da biyu suka jikkata a harin da yan bindiga suka kai da yammacin jiya Lahadi

Rahotanni sun ce maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi tare da kone gidaje.

Wasu bayanai da BBC ta tattara, sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wani sumame da jami’an rundunar kare fararen hula da gwamnatin jihar ta samar suka kai maɓoyar ƴan bindigar, tare da kashe wasu daga cikinsu, da kuma kwashe makamansu, lamarin da ya sa jiya Lahadi, da yamaci, ƴan bindigar suka yi shiri na musamman suka tunkari garin na Nasarawar Zurmi, yayin da mutane ke Shirin yin sallar magariba, kamar yadda wanan mazaunin garin da muka sakaye sunansa, ya shaidawa BBC .

‘‘Muna hira dab da mu yi magriba, kawai sai muka ji ɗa-ɗa-ɗa, ƴan bindiga kawai sun fara harba bindiga yadda ka san tururuwa ta fito. Suka ɗauki hankalin ƴan caji-ofis don muna kusa da caji-ofis, haka suka shigo garin suna kabbara suna harbi kowa ya kama kanshi, ƴan caji-ofis sukai ta ɗauki ba daɗi da su. Cikin ikon Allah mataimakin DPO na yankin shi ma Allah ya amshi ranshi.’’

Mutumin ya ce yana ji yana gani ya tsallake ya bar iyalinsa saboda harbin da ƴan bindigar ke yi ya matuƙar firgita shi, lamarin da ya ce ya tliasta masa neman mafaka a cikin wani gidan ƙaninsa.

Shima wani mazaunin garin na Nasarawar Zurmi, da ya tsallake rijiya da baya, ya ce ƴan bindigar sun yi shiga ne irin ta askarawan da aka yaye a baya bayan nan don kare fararen hula, don haka jama’a sai suka yi tsammanin cewa ba yan bindiga bane.

‘‘Da uniform ɗin su kamar na askarawan ga da aka yaye, sai mutane na ce masu Allah ya kiyaye ku, ba su damu da mutane ba sai da suka shigo gari. To suna fa zuwa bakin police station sai suka fara buɗe wuta, suka sa wa wani waje inda muke wuta, to shi ne babban tashin hankalin da muka fara gani. To sai suka sa wa motar wani Yazidu wuta, suka je gareji suka sanya wa duk wani babur da ke wajen wuta, suka kuma kwashi kaya daga shaguna.’’

A lokuta da dama dai, jami’an tsaro kan ce ba a sanar da su irin wadannan abubuwa da ke faruwa a kan lokaci domin kai agajin gaggawa, to sai dai mutanen garin na Nasarawar Zurmi, sun ce duk da sansanin kar-ta-kwana na rundunar soji da ke kusa da su, waɗanda ba su fito ba domin kare su, sun yin ƙoƙari wajen buga waya domin sanar da ƴan uwansu da ke Gusau, sannan ne wasu sojojin daga Ƙaura suka kawo ɗauki.

Game da wannan al’amari BBC ta yi kokarin jin tabakin mai Magana da yawun rundunar yan sandan Najeriyar a jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, sai dai bai amsa kiraye kirayen waya da aka yi masa ba.

Haka shi ma kakakin gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris, bai amsa waya ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, inda kai hari kan fararen hula ya zama ruwan dare.

Mahukunta dai na cewa suna daukar matakan kawo ƙarshen matsalar to amma a zahiri abin ƙaruwa yake, don haka ne ma wasu ke ganin da sauran rina a kaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here