Home Siyasa Wasika Ga Shugaban Kasa: Da Ta Bulla a Dandalin Sada Zumunta Da...

Wasika Ga Shugaban Kasa: Da Ta Bulla a Dandalin Sada Zumunta Da Ga Gurin Mu Take Sai Dai…? In Ji Sanata Wadada

93
0
Sanata Wadada Kifi

Shugaban Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa Sanata Aliyu Wadada ya ce duk da cewa wasikar da ta bulla a Dandalin Sada Zumunta ba bu rattaba hannun sa akan takardar lallai wannan takarda da ga gurin su ta ke.

Ya sanar da haka ne ga Yanjaridu a jiya Talata a lokacin da ya ke karin haske akan bullar takardar da ta baiyana a kafar Sada Zumunta amma ba bu sa ka hannun sa a kan takardar.

“Eh! tabbas mu muka rubuta wannan takarda da ku ka gani a kafafen Sada Zumunta, sai dai ba bisa umarnin mu a ka buga wannan takarda ba domin ba bu saka hannu na a kan takardar kuma bamu kammala binciken da mu ke yi ba akan batutuwan da su ke kunshe a cikin tarkardar ba. Kwatsam sai mu ka ga ta bulla a Dandalin. Wannan cin amanar aikin Gwamnati ne” In ji Wadada.

Sanata Wadada ya ce rahoton bincikene da su ke yi a kan Kamfanin Mai Na Kasa NNPC ne da kuma Hukumar  tara Haraji ta Kasa wato FIRS wadanda ya ce sun gano cewa akwai biliyoyin Daloli da ba’a sa ka su a asusun Gwamnatin Taraiya. Kuma sun gano cewa ba gaskiya ba ne yawan Mai da ake cewa a na hakowa a Kasarnan yafi abun da a ke sanar da Yan Najeriya a na hakowa.

Y a ce wannan rahoton wacin gadi ne su ka rubuta wasika zuwa ga Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio domin su sanar da su gabanin su gabatar da rahoton su amma kafin su kammala rubuta wasikar wani ya je ya saki wasikar a Dandalin Sada Zumunta.

Sanatan ya amince da duka bayanai da su ke cikin wasikar da ga gurin su take. Har ma akwai karin bayanai wadanda ba su ida rubutawa ba. Sai dai ya yi Allah wadai da wanda ya yi wannan al’amari in da ya ce sun bar shi da Allah na amanar da ya ci na aikin da a ka dora masa.

Wadada y a ce aikin binciken sun bawa wani Kamfani na kwararru ne wadanda ba sa shakkar kwarewar su sai dai duk da ya ke  su na da kwarewa bincike ne wanda bai kammala ba kuma za ‘a iya kalubalantar abun da su ka rubuta tun da ba wahayi bane da ga Allah subhanahu wata’ala.

Da ya ke fadar ra’ayin sa game da bikin cika shekaru 25 da Najeriya ta yi a na mulkin Demokradiyya y a ce har yanzu da sauran rina a kaba domin Shugabannin sun gaza wajen samar da mulki na adalci in da ya bada da misali da albashin ma’akata na N65,000 da ake magana akai ya ce,  ya yi kadan mutuka tun da ko shinkafa buhu guda ba zai sayawa ma’aiaci ba.

Ya ce irin wadannan tsare-tsare wadan da ba na gaskiya ba su su ke bayar da kafa na cinhanci da rashawa da sauran aiyuka na ta’addanci. In da y a kara da cewa rashin bawa kananan Hukumomin Yancin Cin gashin Kai shi ya saka Kasarnan a cikin matsalolin da a ke fuskanta na Tsaro da matsi na tattalin arziki.

Sanata Wadada ya ce idan Allah ya ba shi ikon zama Gwamnan Jihar sa ta Nasarawa abu na farko da zai yi shi ne ya bawa kananan Hukumomi Yancin cin gashin kan su. Wanda hakan ya ce zai kawo bunkasar tattalin arziki da kwanciyar hankali kamar yadda ya ke a baya.

A bangaren nasarori kuma, Sanata Wadada ya ce a cikin shekaru 25 an samu nasarori ma su yawa a fannoni da dama in da ya ce mulkin Demokradiyya ne ya kawo mana wayar Salulu wacce da ita ne a ke gudanar da harkoki da yawa na kasuwanci da sada zumunci.

Har ila yau, ya lissafa cigaban da aka samu ta bangaren gine-gine da samar da asibitoci da makarantu da sauran su. Sai dai ya ce akwai bukatar a kara himma wajen ganin cewa shugabanci ya amfani jama’a ta hanyar yi mu su adalci da samar da ababen more rayuwa wadanda za su inganta rayuwar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here