Home Ilimi Warewa Ilimi Naira Tiriliyan 1.1 A Kasafin Kudi Na 2024 Wata Manuniya...

Warewa Ilimi Naira Tiriliyan 1.1 A Kasafin Kudi Na 2024 Wata Manuniya Ce Na Cigaba A Fannin – Majalisar Taraiya

167
0
Hon. Fulata a

Majalisar Taraiya ta baiyana warewa bangaren Ilimi Naira Tiriliyan 1.1 wato kaso 7 % na Kasafin Kudi na Shekara ta 2024 wata manuniya ce da ke nuna cewa an dauki hanyar gyara na bunkasa ilimi da koyo da koyarwa a Kasarnan.

Shugaban Kwamitin Ilimin Jami’a na Majalisar Wakilai Hon. Abubakar Hassan Fulata Dan Majalisar Taraiya da ke Wakiltar Birniwa da Kirikasamma da Guri da ga Jigawa ne ya baiyana haka a wata hira da Yan Jaridu a ofishin sa da ke Majalisar a ranar Alhamis.

Ya ce wannan kari da ak yi abun a yabawa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne da ya ware wadannan makuden kudade ga fannin Ilimi. Ya ce ko da ya ke hakan ba ya na nufin kudaden sun wadata ba ne amma an samu kari fiye da yadda ake samu a baya.

Hon. Fulata ya ce Majalisar Taraiya za ta yi duk mai yiwuwa wajen saka ido don ganin an kashe wadannan kudade kamar yadda ya kamata.

Har ila yau, Dan Majalisar ya  yabawa Shugaban Kasar da ya amsa kiraye kiraye na Majalisar da sauran Yan Najeriya na cire Jami’o’I da Kwalejojin Ilimi da ga tsarin nan na IPPIS. Ya ce yin hakan ya yi mutukar dacewa ganin yadda aka yiwa harkar Ilimi kanshin mutuwa.

Ya ce sakamakon cire wannan tsari na IPPIS zai bawa Jami’o’I da Kwalejojin ilimi dama da su cigaba da daukar ma’aikata da gudanar da aiyukan su kamar yadda doka ta tanada ba tare da wata matsala ba. Ya kara da cewa kakabawa Jamioin tsarin IPPIS kuskure ne na cewa kada su dauki ko da masinja ne sai sun sami izini da ga hukumomi har 7.

Fulata ya ce Majalisar ta ja hankalin Jamioin da Kwalejojin na Ilimin da su tsaya akan dokokin da suka kafa su tare da bin ka’idoji ta yadda za a cimma burin da aka kafa su. In da ya ce Kwalejojin Ilimi an kafa su ne don su rinka samar da Malamai da za su rinka koyarwa a Sakandare da Firamare, in da su kuma Jamioi an kafa su ne domin su rinka samar da Digiri a fannoni daban daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here