Home Siyasa Wane ne sabon Firaiministan Birtaniya, Keir Starmer?

Wane ne sabon Firaiministan Birtaniya, Keir Starmer?

65
0
Sir Keir 2

Sir Keir Starmer ya zama sabon Firaiministan Birtaniya bayan jagorantar jam’iyyar Labour zuwa ga gagarumar nasarar da ta samu a zaɓen da aka gudanar a ƙasar.

Keir ya maye gurbin Jeremy Corbin a matsayin jagoran jam’iyyar Labour ne shekara huɗu da suka gabata, kuma tun wancan lokacin ne ya yi ta fafutikar ganin jam’iyyar ta ƙara samun goyon baya daga al’umma.

Jam’iyyar Labour ta kwashe shekara 14 ba tare da ta jagoranci gwamnati ba a Birtaniya.

Rayuwarsa kafin shiga siyasa

Sir Keir ya zama ɗan majalisa ne daga baya, lokacin da ya zarta shekara 50 a duniya, bayan ya kwashe shekaru yana aikin lauya.

To amma, a tsawon rayuwar tasa ya kasance mutum ne mai son harkokin siyasa, kuma mutum ne mai son kawo sauyi tun lokacin ƙuruciyarsa.

An haife shi ne a birnin Landan a shekarar 1962 – ɗaya a cikin ƴaƴa huɗu a wurin mahaifinsa – ya girma a yankin Surrey da ke gabashin ƙasar Ingila.

Mahaifinsa ma’aikacin kamfani ne yayin da mahaifiyarsa kuma malamar jinya ce.

Iyayensa sun kasance riƙaƙƙun magoya bayan jam’iyyar Labour.

An raɗa masa sunan Keir ne albarkacin sunan shugaban jam’iyyar Labour na farko, kuma mai haƙar ma’adanai ɗan asalin Scotland, Keir Hardie.

Rayuwar mahaifansa na cike da ruɗani. Sir Keir ya ce mahaifinsa ba mutum ne mai jansu a jiki ba.

Mahaifiyarsa ta yi fama da wata lalurar garkuwar jiki, inda a mafi yawancin rayuwarta ba ta iya tafiya ko kuma magana.

Haka nan lamarin ya kai ga datse mata ƙafa.

Sir Keir ya shiga cikin gungun matasa ƴan jam’iyyar Labour a yankinsa lokacin yana ɗan shekara 16.

Haka nan a wani lokaci na rayuwarsa ya kasance editan jaridar ‘Socialist Alternatives’, mai rajin kawo sauyi.

Sir Keir ne mutum na farko a gidansu da ya taɓa zuwa jami’a. Ya yi karatun harkar shari’a Leeds da Oxford, daga nan sai ya yi aikin lauya a ɓangaren kare hakkin ɗan’adam.

A lokacin da yake harkar lauyanci, ya yi fafutikar ganin an kawar da hukuncin kisa a ƙasashen yankin Karebiya da kuma wasu ƙasashen Afirka.

A wata mashahuriyar shari’a kan ke nufin cewa da aka tafka cikin shekarun 1990, Keir ya kare wasu ƴan gwagwarmayar kare muhalli biyu, waɗanda babban gidan cin abinci na MacDonalds ya shigar da su ƙara bisa zargin ɓata suna.

A shekarar 2008, an naɗa Sir Keir a muƙamin shugaban sashen gabatar da ƙara na Birtaniya, wanda hakan na nufin babu wani mai gabatar da ƙara a Ingila da Wales sama da shi.

Ya riƙe muƙamin har zuwa shekarar 2013, kuma masarautar Birtaniya ta karrama shi da ɗaya daga cikin lambar yabo mafiya daraja a shekarar 2014.

Sir Keir ne mutum na farko a gidansu da ya taɓa zuwa jami’a. Ya yi karatun harkar shari’a Leeds da Oxford, daga nan sai ya yi aikin lauya a ɓangaren kare hakkin ɗan’adam.

A lokacin da yake harkar lauyanci, ya yi fafutikar ganin an kawar da hukuncin kisa a ƙasashen yankin Karebiya da kuma wasu ƙasashen Afirka.

A wata mashahuriyar shari’a kan ke nufin cewa da aka tafka cikin shekarun 1990, Keir ya kare wasu ƴan gwagwarmayar kare muhalli biyu, waɗanda babban gidan cin abinci na MacDonalds ya shigar da su ƙara bisa zargin ɓata suna.

A shekarar 2008, an naɗa Sir Keir a muƙamin shugaban sashen gabatar da ƙara na Birtaniya, wanda hakan na nufin babu wani mai gabatar da ƙara a Ingila da Wales sama da shi.

Ya riƙe muƙamin har zuwa shekarar 2013, kuma masarautar Birtaniya ta karrama shi da ɗaya daga cikin lambar yabo mafiya daraja a shekarar 2014.

Zama shugaban jam’iyya Labour

Sir Keir ya je majalisar dokoki ne a shekarar 2015, a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar yankin Holborn da St Pancras a Landan.

Jam’iyyar Labour ta kasance a ɓangaren adawa a lokacin jagorancin Jeremy Corbyn.

Ya bai wa Sir Kier muƙamin ministan jam’iyyar hamayya kan harkokin cikin gida, wanda ke sanya ido sosai kan ayyukan gwamnati a ɓangaren lamurra kamar na shige da fice.

Bayan da Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai, an naɗa Sir Keir a matsayin sakataren jam’iyyar hamayya kan shirin ficewar ƙasar daga Tarayyar Turai.

Ya yi amfani da muƙamin nasa wajen ƙoƙarin ganin an gudanar da ƙuri’ar jin ra’ayin al’umma a karo na biyu.

Sir Keir ya samu damar zama jagoran jam’iyyar Labour ne bayan babban zaɓen Birtaniya na 2019.

Sakamakon zaɓen bai yi wa jam’iyyar daɗi ba kwata-kwata – shi ne rashin nasara mafi muni da ta samu tun shekarar 1935 – hakan ya tilasta wa Jeremy Corbyn sauka daga muƙaminsa.

Daga nan ne Sir Keir ya yi nasarar zama shugaba tare da yin wasu alƙawurra, waɗanda suka haɗa da karatun jami’a kyauta.

Jagorancin Corbyn ya rarraba kan ƴaƴan jam’iyyar.

Shi kuwa Sir Keir ya ce manufarsa ita ce haɗe kan jam’iyyar, amma zai ɗora kan “tsattsauran” aƙidar Jeremy Corbyn.

Tun daga wancan lokaci ne Sir Keir ya sa aka dakatar da Jeremy Corbyn daga jam’iyyar Labour a majalisa sanadiyyar saɓani da aka samu kan ƙin jinin Yahudawa, wanda aka riƙa taƙaddama a kai lokacin jagorancin Mista Corbyn.

Da dama daga cikin ƴaƴan jam’iyyar masu ra’ayin sauyi sun ce Sir Keir ya riƙa shiri na dogon zango ta hanyar tabbatar da cewa ƴaƴan jam’iyyar masu matsakaicin ra’yin sauyi ne kawai ke tsayawa takarar majalisar dokoki.

Mene ne ra’ayin Sir Keir kan… ?

Duk da irin abubuwan da ya fada a lokacin da yake kokarin zama jagoran jam’iyyarsa, Sir Keir ya yi kokarin karkata akalar jam’iyyar zuwa mai matsakaicin ra’ayi ta yadda za ta samu karin goyon baya.

Ya yi watsi da wasu manufofin jam’iyyar masu tsada, inda ya kafa hujja da halin rashin kudi da kasar ke ciki, sai dai ya ci gaba da riko da wasu tsauraran shirye-shirye.

Sir Keir 4

Mayar da komai hannun ‘yan kasa

Sir Keir ya dakatar da shawarwarinsa na farko kan mayar da harkar samar da makamashi da ruwa ga kamfanonin yan kasa.

Sai dai ya yi alkawarin cewa zai mayar da kusan dukkanin harkar sufurin jiragen kasa na kasar a hannun gwamnati cikin shekara biyar, karkashin wani sabon kamfani da za a kira shi Kamfanin sufurin jiragen kasa na Birtaniya.

Ilimi

Sir Keir ya yi watsi da alkawarinsa na farko kan cewa karatun jami’a zai zama kyauta, inda ya ce gwamnati ba za ta iya daukar nauyin hakan ba.

A watan Mayu ya shaida wa BBC cewa: “Akwai yiwuwar mu sauya shawara kan wannan batu saboda mun samu kanmu cikin wani yanayi na rashin kudi.”

Sai dai Sir Keir ya ce gwamnatin Jam’iyyar Labour za ta rika karbar harajin hada-hadar kudi kan kudin makaranta na makarantu masu zaman kansu.

Muhalli

Jam’iyyar Labour ta zabtare alkawarin da ta dauka a 2021 na cewa za ta kashe fan biliyan 28 a shekara daya kan shirye-shiryen samar da tsaftataccen makamashi, sai dai ya ce zai dore da shirye-shiryen samar da cibiyoyin samar da lantarki ta hanyar iska da kuma bangaren samar da baturan motoci masu amfani da lantarki.

Wannan ya janyo masa suka daga ‘yayan jam’iyyar Conservatives, wadanda ke zargin shi da kokarin “zulle” wa wasu manyan alkawurra da ya dauka.

A baya-bayan nan Sir Keir ya dauki alkawarin zuba jarin kudi fan biliyan takwas a bangaren tsaftataccen makamashi ta hanyar wani kamfani da ake kira GB Energy.

Haka nan ya yi alkawarin kawar da amfani da abubuwa masu gurbata muhalli wajen samar da makamashi wajen samar da lantarki a Birtaniya, nan da shekara ta 2030.

Masana da dama na ganin cewa wannan ba abu ne mai yiwuwa ba.

Isra’ila da Gaza

Bayan harin da Hamas ta kai wa Isra’ila a watan Oktoban 2023, Sir Keir ya goyi bayan matakan da Isra’ila ke dauka a Gaza da kuma ‘yancinta na kare kai.

Wannan lamari ya fusata ‘yan kasar da dama masu goyon bayan Falasdinawa, kuma ya fuskanci bore daga gwamman ‘yan majalisar jam’iyyar ta Labour wadanda suka yi kira da a tsagaita wuta nan take.

Sai dai a watan Fabarairun wannan shekara ya yi kiran a samu “tsagaita wuta mai dorewa. Abu ne da ake bukata nan take”.

Wata kuri’ar jin ra’ayin al’umma na YouGov da aka gudanar a watan Maris ya nuna cewa kashi 52 cikin dari na al’ummar Birtaniya na ganin bai yi abin da ya kamata ba game da lamarin.

Haka nan kuma Sir Keir ya goyi bayan matakin Birtaniya na yin ruwan bama-bamai kan sansanonin mayakan Houthi a Yemen bayan harin da kungiyar ta kai kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila.

Nahiyar Turai

A 2019, Sir Keir ya tursasa aka yi zaben jin ra’ayin al’umma karo na biyu kan ko ya kamata Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai.

Yanzu ya ce babu batun sauya akalar kasar daga matakin da ta dauka na ficewa daga Tarayyar Turai, amma ya ce zai tattauna kan sabbin yarjeniyoyin hadin gwiwa da kasashen Tarayyar Turai game da abinci da muhalli da kuma abin da ya shafi kwadago.

Sir Keir 3

‘Na tsani rashin nasara’

Wasu yan adawarsa na bayyana Sir Keir Starmer a matsayin mara kuzari.

Yana son nuna kansa a matsayin mai riko da doka, wani abokinsa ya bayyana shi a matsayin sarkin son bin doka.

Sau daya kawai ya taba saba doka. A lokacin da yake matashi, ‘yansanda sun kama shi da laifin sayar da askirim ba tare da izini ba.

An kwace askirim din amma babu wani hikunci da aka yi masa.

Bai cika son yin bayani game da rayuwarsa ba a lokacin tattaunawa da ‘yan jarida

Ya taba fada wa wata jaridar Birtaniya ma suna ‘Guardin’: “Na tsani rashin masara. Wasu na cewa shiga a dama da kai ma wani abu ne. Ba na cikin irin wadannan.“

Sir Keir ya auri matarsa Victoria Alexander- wadda ke aiki a Hukumar lafiya ta Birtaniya- a shekarar 2007. Suna da ‘yaya biyu.

Yakan yi kwallo domin nishadi kuma shi mai goyon bayan kungiyar Arsenal ne. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here