Home Ilimi Uwargidan gwamna Ganduje, Hafsat, ta kirkiro wa Kanawa sabon ‘Take’ da za...

Uwargidan gwamna Ganduje, Hafsat, ta kirkiro wa Kanawa sabon ‘Take’ da za a rika rerawa

264
0

Gwamna Ganduje ya ce an yi ‘Take’ ne domin a saka kishin kasa da kuma nuna Kano a matsayin babbar cibiyar kasuwanci da al’adu da jagoranci da sauran kyawawan halaye.

A wata sanarwa da Abba Anwar mai magana da yawun gwamna Ganduje ya fitar, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ci gaba da kiyaye tarihi, al’adu da kasuwanci na jihar, domin ci gaban kasa baki daya.

Gwamnan ya yaba da jinjina wa uwargidansa Hafsat Ganduje, wanda ita ce ta hassasa kirkiro da wannan waka don cigabar jihar.

” Abinda da mai daki na ta yi na kirkiro wannan waka abin a yaba ne. Mu na godiya kuma da zarar an kammala aiki akan sa a majalisa, za a fara amfani da shi a jihar.

” Za mu mika wannan waka zuwa majalisar jihar domin ya zama doka. Idan aka zo taro duk lokacin da aka rera taken Najeriya sai kuma a rera ta jihar Kano. (Premium Times).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here