Home Tsaro Tura Sojoji Nijar: Zai Kara Jefa Najeriya Cikin Mawuyacin Hali – Inji...

Tura Sojoji Nijar: Zai Kara Jefa Najeriya Cikin Mawuyacin Hali – Inji Sanata Hanga

232
0
Service Chiefs with Tinubu

Tura Sojojin Najeriya zuwa yaki Kasar Nijar zai kara jefa Najeriya cikin matsi na tattalin arziki da asarar rayuka da dukiya mai yawa ; wanda hakan bai da ce ba a wannan lokaci da muke ciki in Sanata Rufai Hanga Danmajlisar Taraiya da ke Wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya.

Sanata Hanga ya fadi Haka ne a hirarsa da Jaridar Viewfinder a ofishinsa da ke Abuja in ya kara da cewa Shugaban Kasar ya karya dokar Majalisar Taraiya idan har ya aiwatar da kudurinsa ba tare da samun amincewar Majalisar ba.

Sanata Abdul Ningi ne ya jawo hankalin Majalisar akan Wasikar Shugaban Kasar in da ya ce, bai kamata Shugaban ya bawa  Majalisar Labarin aniyar sa ba, abun da ya kamata ya yi shine ya turowa da Majalisar bukatarsa sannan Majalisar ta yi mahawara akai kafin ta amince da bukatar ta sa inji Sanata Hanga.

A nasa bangaren Sanata Abdul Ningi ya karawa Viewfindeer haske inda ya ce Dokar Majalisar ta ne mi Shugaban Kasa da ya nemi sahalewar ta kafin a shiga yaki da kowacce kasa ba wai a bawa Majalisa Labari ba cewa za a shiga yaki ko kuma a shiga yaki gadan gadan.

Sanata Ningi ya ce “bai kamata mu shiga yaki ba kawai sabo da muna so mu marawa Nijar baya ya kamata mu lura da abubuwan da ka je su zo”. In da ya ce tuni wasu kasashe irin su Barkinafaso da Russia sun marawa Sojojin Nijar baya sabo da haka akwai hadari idan Najeriya ta shiga fadan ba tare da  ta yi nazari akai ba.

Ningi ya kara da cewa akwai bukatar mu yi nazari akan halin da Jihohi da ke kan iya ka za su shiga kamar su Katsina da Jigawa da kuma tanadi da za a yin a muhallin da zasu koma idan yaki ya runcabe da bukatun su na muhalli da abinci da sauran bukatu.

Har ila yau, ya ce tuni Najeriya tana fama da yaki da yan ta’adda acikin gida kuma an rasa Sojoji masu yawa bayan Najeriya bata da isassun jami’an tsaro a kasarnan sabo da haka Majalisar Taraiya ba zata amince da a shiga yaki da wata kasa ba a wannan lokaci inji Abdul Ningi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here