Home Kotu da 'Yan sanda Tuhume-Tuhumen Kan Alhassan Doguwa Masana Sun Fara Sharhi Kan Batum

Tuhume-Tuhumen Kan Alhassan Doguwa Masana Sun Fara Sharhi Kan Batum

264
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan kasar Alhassan Ado Doguwa a gaban kotun majistire ta jihar, bisa tuhumar sa da hannu a tarzomar zabe, inda wasu mutane uku suka rasa rayukansu a yankin mazabarsa.

Mallaka da amfani da makami babu izini, tsarawa da hada baki wajen aikata miyagun laifuka, kisan kai da kuma tada hankalin jama’a, suna daga cikin abubuwan da aka tuhumi Alhassan Ado Doguwa a zauren kotun.

Lauya mai gabatar da kara Barrister A’isha Salisu, tace rahotan farko na binciken ‘yan sanda ya nuna akwai zargi akan Alhassan Ado Doguwa, na cewa ya hada baki da wani mai suna Bashir Dahiru na kauyen Jammaje, da Bala mai Doki, da Hamisu Musa, da Nazifi Asananic, da Abdullahi Haruna, da kuma karin wasu da dama da yanzu haka ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo bayan da aka ce sun tada fitina ta hanyar cinna wuta a sakatariyar NNPP ta karamar hukumar Tudunwada ta yankin kudancin Kano.

Kazalika, ana tuhumar Alhassan Ado Doguwa da raunata wani mai suna Alhassan Muhammad Sarkin Fawa da wasu mutane da dama, kana ya harbi wani Ibrahim Danbala, bayan haka ya jikkata wani Auwal Dauda ya kuma raunata wasu mutane da wuka.

Tun da fari dai Alhassan Ado Doguwa ya fada wa kotu cewa, yana muradin a karanto masa tuhume-tuhumen da harshen Hausa zalla maimakon yaren turanci, bukatar da kotun ta amince da ita nan take.

Daga bisani dai lauyan Alhassan Ado Doguwa Barr Abdul Adamu, ya roki kotun ta bashi belinsa, la’akari da matsayinsa a majalisar wakilan Najeriya, amma Barr Aisha Salisu ta soki yunkurin bada belin.

Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim Mansur Yola, ya bada umurnin a tsare Alhassan Ado Doguwa a gidan Kurkuku. Yana mai cewa la’akari da girman laifukan da ake tuhumar dan majalisar tarayyar, kotunsa ba ta da hurumin yin shari’ar, amma ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga wannan wata na Maris, kuma ana sa ran gabanin lokacin an sami karin bayanai da shawarwari daga ma’aikatar shari’a ta jihar Kano.

Yanzu haka dai masana a fannoni dabamdaban na tsokaci akan wannan batu.

Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce matakin ya fara nuna cewa ‘yan sanda sun fara yin aikin su yadda ya kamata kuma hakan zai zama darasi ga ‘yan siyasar da ke sha’awar yin abin da ake zargin shi Alhassan Ado Doguwa da aikatawa.

Shi kuwa lauyan kare hakkin bil’adama Dr. Audu Bulama Bukarti, cewa yayi abin da ‘yan sandan suka yi na gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu yana da kyau, amma sai bayan an tabbatar da hukuncin daya dace akansa bayan an tabbatar da laifi, san nan ne za a yaba wa ‘yan sanda da alkalai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here