Home Siyasa Tshige Buhari: Yan Majalisa kubi a Hankali – inji Kwankwaso

Tshige Buhari: Yan Majalisa kubi a Hankali – inji Kwankwaso

162
0

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ja hankalin wasu daga cikin ‘yan majalisa kan su bi a hankali wajen neman tsige shugaba, Muhammadu Buhari.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta rawaito cewa Kwanwaso ya faɗi hakan ne a Ilorin a ziyarar da ya kai wa gwamna ABdulRahman AbdulRazaq.
Sanata Kwankwaso na cewa kada ‘yan majalisa su yi gaggawa wajen aiwatar da matakinsu.
Ɗan takarar ya ce babu shaka akwai damuwa matuƙa kan halin da tsaron ƙasa ke ciki tare da shawarta gwamnati ta dau wannan a matsayin babban kalubale a gareta.
Kwankwaso, wanda tsohon ministan tsaro ne, ya roƙi gwamnati ta yi harama wajen sauraren koken al’umma da shawo kan matsalolin da suka addabesu.
Kwankwaso na wannan ziyarar ne a Ilorin domin bude sabuwar ofishin NNPP da kuma na sauran jihohi makwabta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here