Home Siyasa TONON SILILI: An bankaɗo kantama-kantaman gidaje 20 da Tinubu ya saya a...

TONON SILILI: An bankaɗo kantama-kantaman gidaje 20 da Tinubu ya saya a Landan, lokacin ya na gwamnan Legas

195
0

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa na Najeriya, Bola Tinubu, wanda a yanzu haka jam’iyyu shida su ka maka shi kotu su na neman kada a rantsar da shi, an gano yadda ya kimshe kaso mai tsoka na dukiyar da ya mallaka a Ingila.

A Landan dai an bankaɗo wasu kantama-kantaman gidaje da aka tabbatar ko dai mallakar sa ne shi kaɗai, har gidaje 20, ko kuma har da makusantan sa.

An kuma gano cewa an sayi gidajen ne a lokacin da Tinubu ke Gwamnan Jihar Legas.

Tinubu wanda za a rantsar a ranar 29 Ga Mayu, 2023, shi ne zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari. Masu adawa da shi dai na ganin cewa zaɓen Tinubu ba sahihi ba ne, shiri ne kawai.

Tinubu wanda ya zama ubangidan ‘yan siyasa da dama a Kudu maso Yamma, musamman gwamnonin su da ya riƙa ɗaure wa gindi su na hawa mulki, ana kuma yi masa kallon mutumin da ya taimaka wa Buhari ya yi nasarar zama shugaban ƙasa a zaɓen 2015 da 2019.

Yawancin waɗanda ya riƙa ɗaure wa gindi su na zama gwamnoni, tsoffin Daraktoci ne a kamfanin Tinubu da ɗan sa.

Jaridar Blooberg dai a ranar Talata ta buga labarin cewa ɗan Bola Tinubu mai suna Oluwaseyi, shi ne mai gaba ɗayan hannun jarin kamfanin Aranda Overseas Corporation, kamfanin ƙasar waje, wanda ya sayi kadarorin dala miliyan 19.8 a Ingila, cikin 2017.

A daidai lokacin da aka sayi gidan kuwa, Najeriya na ta gaganiyar ganin ta ƙwace wani katafaren gida a Landan, mallakar wani wani ɗan ƙaƙudubar dillalin ɗanyen fetur, wanda ke fuskantar tuhumar cajin sa da zamba da rashawa a Najeriya da Biritaniya.

OCCRP, kafar yaɗa labarai mai yarjejeniyar musayar muhimman bayanan sirri da PREMIUM TIMES ce ta sanar da wannan jarida duk ababen da binne , amma aka bankaɗo su kwanan nan.

OCCRP ta ƙara bankaɗo wasu gidajen kimanin 20 a Landan, waɗanda ke da alaƙa da Tinubu.

Kafar ta kuma jaddada cewa an sayi gidajen da a lokacin da Tinubu ke Gwamnan Jihar Legas, tsakanin Mayu 1999 zuwa Mayu 2007.

Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu dai bai amsa kiran wayar da wakilin mu ba, domin jin ta bakin Tinubu.

‘Akwai Buƙatar A Binciki Inda Aka Samo Kuɗaɗen Da Aka Sayi Gidajen’ – TI

Ƙungiyar Bin Diddiƙin Fassala Kuɗaɗen Sata Da Toshi Rashawa (Transparency International) ta Birtaniya, ta ce idan akwai alamomin da ke nuna cewa an sayi gidajen da “kuɗaɗen sata, to a binciki kuɗaɗen.” Haka dai Shugaban Sashen Bincike na TI, Steve Goodrich ya bayyana.

“Saboda zai yi wahala haka kawai ya tattago maƙudan kuɗaɗe a sayi kantama-kantaman gidaje da su a Landan, sai fa an yi hakan ne kawai da nufin ɓoye wata ɓarna.” Inji shi.

Tarihin Dagwalon Dattin Harƙallar Tinubu:

  1. Cikin 1993 Gwamnatin Amurka ta tilasta shi ya yi aman dala 460,00, matsayin kuɗaɗen cinikin harƙallar muggan ƙwayoyi da Amurka ta kama Tinubu ya shiga ƙasar da ƙwayar.

Kotun Gundumar Illinois da ke Amurka ce ta yanke masa wannan hukunci a cikin 1993.

  1. Cikin 1993 ɗin dai, wani kamfani mallakar Tinubu mai Abeeb Holdings Limited, da ke ƙasar waje, mai rajistar a Tsibirin Gibraltar, ya sayi gida mai lamba ‘Flat 9, kan Titin New Cavendish a Landan.

Gwamnatin Birtaniya ce ta gano wanda ya mallaki gidan, ta hanyar gano sunan mai kamfanin a ƙarƙashin wata sabuwar dokar Bayyana Sunayen Masu Rajistar Kamfanoni A Ƙasashen Waje.

  1. Cikin 2011 kuma kamfanin Aranda Overseas Corporation, mallakar ɗan Bola Tinubu, ya sayi gida mai lamba 10A, kusa da gidan da Tinubu ya saya cikin 1993.

Wani makusancin Tinubu mai suna Oladipo Eludoyin, wanda Darakta ne a kamfanin Aranda Overseas Corporation ya sa hannu kan takardun cinikin gidan.

  1. OCCRP ya fallasa cewa Eludoyin ne mai wasu gidaje 17 da aka saya a ƙarƙashin wasu kuɗaɗen da aka biya daga kamfanoni uku na Tsiribin British Virgin Islands. Gidajen 17 a Landan aka saye su.
  2. Gidajen waɗanda Eludoyin ya saya a cikin 2004 da 2007, an saye su ne lokacin Tinubu ya na gwamna a Jihar Legas.

Babatunde Fashola wanda ya yi gwamna bayan saukar Tinubu a Legas da Gwamna Sanwo-Olu na yanzu, duk sun taɓa yin aiki a ƙarƙashin kamfanin Aranda Resou Limited.

Domin shi Sanwo-Olu ma bai yi ritaya daga muƙamin Darakta a Aranda Resources Limited na Tinubu ba, sai ana saura kwanaki 26 a rantsar da shi gwamnan Legas.

Shi ma tsohon Gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola ya taɓa riƙe muƙamin Darakta a Aranda Overseas Corporation.

Ba a dai san lokacin da ɗan gidan Tinubu ya mallaki kamfanin Aranda Overseas Corporation ba. Amma dai a 1999 lokacin da aka yi wa kamfanin lasisin haɗewa a British Virgin Islands, ɗan gidan Tinubu ya na da shekaru 14, kuma a shekarar aka saka shi sakandare ta Milton Abbey a Ingila

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here